Shirin kammala yakin zabe a Tunisiya | Labarai | DW | 19.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin kammala yakin zabe a Tunisiya

A wannan Jumma'a ce ake kawo karshe yakin neman zabe a Tunisiya, a shirye-shiryen da ake yi na gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a ranar Lahadi mai zuwa.

Akalla 'yan kasar Tunisiya kusan Milian biyar ne da dubu dari uku, suka cancanci su yi zabe. Tuni ma 'yan kasar ta dake kasashen ketare suka fara kada kuri'unsu tun daga wannan Jumma'a.

Za su zabi tsakanin 'yan takara biyu da suka hada da shugaban kasar mai barin gado Moncef Marzouki, da kuma Béji Caïd Essebsi, da yazo na daya a zaben shugaban kasar zagaye na farko. 'Yan takarar biyu dai sun shirya gudanar da wasu manya-manyan tarurrukan gangami a yammacin wannan Jumma'a a Tunis babban birnin kasar ta Tunisiya.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu