1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Rikici a fagen kwallon kafar Turai

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
April 19, 2021

Rikici ya kunno kai a fagen kwallon kafar Turai game da aniyar wasu kungiyoyin Ingila da Spain da Italiya na kafa gasar "Super League" da za ta yi hamayya da Champions league.

https://p.dw.com/p/3sEld
Großbritannien Schals der englischen Fußball-Premier-League-Teams
Hoto: Alastair Grant/AP Photo/picture alliance

Kungiyoyi 12 da ke fada a ji a lig din kasashen Ingila da Spain da Italiya sun ba da sanarwar kirkirar sabuwar gasar kwallon kafa ta Turai mai lakabin "Super League", wacce za ta zama kishiya ga gasar zakarun Turai ta Champions League. Tuni ma suka rufe kofa ga kungiyoyin kasashen Jamus da Faransa, lamarin da ka iya kaiwa ga murkushe gasar zakarun Turai. Sai dai hukumar kwallon kafa ta kasashen Turai wato UEFA ta nuna adawa da wannan yunkurin, wanda ta danganta shi da "son-kai", tare da shan alwashin yakarsa ta duk hanyoyin da suka dace. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da UEFA, kungiyar da ke kula da kwallon kafa ta Turai, ke shirye-shiryen gabatar da shirinta na sake fasalin babbar gasarta ta zakarun Turai, inda maimakon kungiyoyin 32, za ta fara jerawa da 36, wadanda za a rarraba su a rukunoni hudu.

Masu neman ballewa daga gasar kofin zakarun Turai suka ce ta rasa armashin da take da shi a baya, sannan ba ta samar da kudin shiga sosai a yanzu. Sai dai kungiyoyin Faransa da Jamus sun nuna mamakin yadda aka mayar da su saniyar ware a shirin kafa "Super League". Manyan kungiyoyin Turai da suka juya wa shirin UEFA baya, inda suke son sabon zubi na gasa tsakanin kungiyoyi mafi daraja, a mafi samun nasarar cin kofi, kuma mafi wadatar masu gida rana. An ambato kungiyoyin Ingila shida a cikin wannan sabon tsarin gasa ciki har da Arsenal, Chelsea, Liverpool, Manchester City, Manchester United da Tottenham, sai kuma  kungiyoyin Spain uku  wato Atlético de Madrid, FC Barcelona da Real Madrid, yayin da ake da kungiyoyin Italiya guda uku wato da AC Milan, Inter Milan da Juventus. Wadannan kungiyoyi 12 su kadai sun lashe kofin zakarun Turai sau 40 daga cikin karo 66 da suka gudana.

Karawa tsakanin VfL Wolfsburg da Bayern Munich
Karawa tsakanin VfL Wolfsburg da Bayern MunichHoto: Martin Rose/Getty Images

A nan Jamus, an gudanar da wasannin mako na 29 na Bundesliga, inda da gumin goshi Bayern Munich ta doke Wolfsburg da 3-2, a daidai lokacin Yaya Babba na wahalar samun nasarori a baya-bayan nan sakamakon rauni da dodon raga Robert Lewandowski da Leon Goretzka suka fama da shi. Duk da cewa ba ta da tabbacin zama zakara a baya, amma har yanzu Bayern na saman teburi da maki 68.

A yanzu dai Bayern Muncih ta yi wa RB Leipzig ratar maki bakwai, saboda 'yan Leipzig din ta tashi 0-0 a fafatwar da suka yi da Hoffenheim, wanda ke a matsayi na 12 a Bundesliga.

A nata bangaren, Yaya Karama Borussia Dortmund, ta rage ratar da ke tsakanin da Eintracht Frankfurt da ke matsayi na 4, bayan da ta sami nasarar 4-1 a kan Werder Bremen ciki har da kwallaye biyu daga Erling Haaland ya zira. A daidai wannan lokacin, takwararta Borussia Mönchengladbach ta lallasa Frankfurt da ci 4-0. A yanzu dai maki hudu ne kawa ke raba Kungiyoyin frankfurt da Dortmund

Ahmed Musa a wasan sada zumunta tsakanin Najeriya da Ingila a London a watan Yunin 2018
Ahmed Musa a wasan sada zumunta tsakanin Najeriya da Ingila a London a watan Yunin 2018Hoto: Getty Images/AFP/I. Kington

Yayin da shahararen dan wasa Najeriya mai bugawa a nahiyar Turai da asiya Ahmed Musa ya koma gida domin buga wa Kano Pillars Kwallo a matsayin lamba 7, magoya bayan kungiyar na bayyana farin cikinsu ganin yadda dan wasan ke da farin jini a Najeriya. Duk da cewa Ahmed Musa zai shafe watanni biyu ne kacal a Kano Pillars, amma zuwan nasa zai iya kara wa kungiyar ta kano kwarin gwiwar lashe gasar premier lig ta bana.

Yanzu kuma sai fagen boxing, inda Abdul Razak Alhassan dan kasar Ghana ya sha bugu tamkar kuran roko a ranar Asabar a damben matsakaicin ajin da ya yi da Jacob Malkoun a Las Vegas 24, a daura da karon batta da ya gudana tsakanin Robert Whittaker da Kelvin Gastelum. Dukkanin alkalan da suka sa ido a damben Alhassan da Malkoun sun bayyana cewa dan kasar ta Ghana ya samu maki 27 yayin da abokin hamayyarsa ke da 30. Mugunyar kisa ta uku ke nan Abdul Razak Alhassan ya sha a cikin watanni takwas baya ga bugu da ya sha daga Mouniz Lazzez a watan Yuli da kuma ta Khaos Williams a watan Nuwamba. Wannan yana nufin cewa dan dambe Alhassan yana da nasarori 10 yayin da aka doke shi sau hudu.