1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Ji Ka Ƙaru Podcast

Zainab MohammedJanuary 31, 2012

Shirin DW Rediyo na ilimantarwa wa nahiyar Afirka. Waɗanda Suka kunshi wasannin kwaikwayo da bayanai a kan Siyasa da Kiwon lafiya daTattali da Zamantakewa.

https://p.dw.com/p/MpPc
Hoto: DW

Siyasa da Rayuwa

Siyasa na taka muhimmiyar rawa a rayuwar al'umma a Afirka. Mutane da dama na iƙirarin cewar duka-duka abin da ƙasashen Afurka ke buƙata shi ne shugabanci na gari – shugabannin da zasu yi amfani da ikonsu wajen yaƙar talauci da samar da zaman lafiya da ci gaba ga nahiyar. A wannan karon shirin Ji Ka Ƙaru zai yi amfani da wani kyakkyawan salo mai burgewa wajen kawo muku cikakkun bayanai a game da yadda siyasa ke tafiya a Afirka.

Learning by Ear - Political Education and Participation - Getting involved
Hoto: gettyimages

Tattalin Arziki da Muhalli

Shirin Ji Ka Ƙaru zai yi bulaguro da ku domin fahimtar al'amura masu sarƙaƙiya da ban ta'ajibi a dunƙulalliyar duniyar nan ta mu a cikin ƙarni na 21. A cikin salsalar shirye-shiryenmu akan tattalin arziki da muhalli zamu ga yadda Afirka ke tasiri, take kuma samun tasiri a rayuwa ta yau da kullum a duniyar nan ta mu. Misali wasan kwaikwayonmu na rediyo akan tattalin arziki yana ba da haske akan yadda al'amuran tattalin arziki na cikin gida da na ƙetare ke tafiya. Zamu bi diddigin fara harkar kasuwanci daga karamin mataki zuwa hada-hadar cinikin ƙetare.

Learning by Ear - Economy
Hoto: LAI F

Kiwon Lafiya da Zamantakewa

Maganar kiwon lafiya da riga kafi tana da muhimmanci ga kowa-da-kowa, musamman ma a yankunan da ake fama da matsaloli na rayuwa da rashin nagartaccen tsarin kiwon lafiya. Shirin wasan kwaikwayo na Ji Ka Ƙaru akan zazzaɓin cizon sauro da HIV/AIDS zai ba da cikakken bayani game da waɗannan cututtuka guda biyu. Zaku samu damar yi wa masu wasan kwaikwayon rakiya. Kuma mai yiwuwa ku amince da shawararsu ko kuma ku yi watsi da ita.

Learning by Ear - HIV/Aids - Preventing the plague
Hoto: laif

Harkar Ilimi

Da yawa daga matasan Afirka na famar neman kyautata makomarsu a dunƙulalliyar duniyar nan tamu da ta dogara akan ilimi suna kuma tababa a game da hanyar da zata kai su ga nasara a sana'a ko kuma ilimin da suka sa gaba. Shirin Ji Ka Ƙaru zai kutsa da ku cikin harkokin rayuwa ta yau da kullum sannan ya ba ku shawarwari masu ma'ana. Shirin zai duƙufa akan sabuwar fasahar yaɗa labarai, neman ilimi ta yanar gizo da kuma damar samun aiki. Zai kuma tabbatar muku da cewar duniyar nan ta mu na cike da abubuwa na ban mamaki.

Learning by Ear - Computer and the Internet - Closing the digital divide
Hoto: CORBIS