SHIRIN INGANTA HULDA TSAKANIN DALIBAN KETARE DA NA JAMUS NA SAMUN BUNKASA | Siyasa | DW | 29.12.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SHIRIN INGANTA HULDA TSAKANIN DALIBAN KETARE DA NA JAMUS NA SAMUN BUNKASA

Ban da azuzuwa, babu dai inda dalibai suka fi halarta kamar gidajen cin abinci da na shakatawa. A nan ne kuwa suka fi samun damar kulla huldodi tsakaninsu a sawwake. Sabili da haka ne kuwa, a shirin da jami'ar Bonn ta gabatar na inganta tuntubar juna tsakanin dalibai Jamusawa da takwarorinsu da suka zo daga kasashen ketare, ta zabi wasu mashayai na birnin, inda daliban za su iya saduwa da juna, a wasu lolkuta musamman da aka kebe musu. A wadannan lokutan, za su iya sayyen kayayyakin sha a farashi mai sauki.

Kim Vuong, wata daliba daga kasar Kyanada, wadda tun shekara daya da ta wuce ne take karatu a jami'ar Bonn, ta bayyana cewa, za ta taimaka wajen aiwatad da shirin, saboda muhimmancin da ta ga yana da shi:

"A lokacin da na zo nan Jamus, sai na ga kome ya canza mini. Ban san mutane da yawa ba. Na yi begen samun wani, wanda zai iya taimaka mini, wajen warware wasu matsalolin da ko wane bako ke huskanta, a farkon watannin isowarsa a nan Jamus. Ban dai yi sa'ar samun wannan damar ba. Amma yanzu da na saba da halin rayuwa a nan, na kuma gogu da shi, zan iya taimaka wa sabbin daliban da suka zo ba da dadewa ba. Ni dai ina farin cikin saduwa da mutane daga kasashe daban-daban, saboda dukkanmu za mu iya karuwa da wasu al'adu da harsuna da dai sauran ababan da ba namu ba."

Tun shekara ta 2000 ne jami'ar Bonn ta gabatad da nata shirin, da yin kwaikwayo da wani shirin da jami'ar Dortmund ta fara gabatarwa a shekarun baya. A halin yanzu dai, mafi yawan jami'o'in Jamus sun bi sahun jami'o'in biyu, wajen gabatad nasu makamantan shirye-shiryen. A galibi dai, ana kulla huldodi ne tsakanin daliban ketaren da na nan Jamus, ta hanyar gano abin da abokan huldar suka fi sha'awa a kansu, kamar dai yadda Carina Johnen ta bayyanar:

"Abokiyar huldata ce Celine daga Faransa. Ni ma na koyi farasanci, kuma na yi zaman shekara daya a Faransan. Sabili da haka, muna begen ganin junanmu a ko yaushe. Idan ko muka sadu, muna iya tadi a cikin jamusanci ko kuma farasanci. A nawa ganin dai, hakan na da muhimmanci kwarai, saboda muna musayar al'adu, mu kuma nakalci wasu ababan da ba mu sani ba daga juna."

A cikin watanni 6 da súka wuce dai, an sami karin yawan dalibai dari da 22, wadanda suka shiga cikin shirin. Abin ban sha'awa shi ne ganin yadda dalibai daga kasashe kamarsu Madagaskar, da Runada da kuma Bangladesh ke hulda da junansu da kuma takwarorinsu na nan Jamus. dalibai Jamusawa da suka shiga cikin shirin dai sun nuna gamsuwarsu da irin goguwar da suka yi da daliban ketare. Wasu sun bayyana cewa, irin wadannan huldodin za su iya karko su zamo wani ginshiki na inganta fahimtar juna tsakanin al'ummomin duniya. Goreon Koch, wani dalibi bajamushe, na jami'ar ta Bonn, amma wanda ke zaune a birnin Kwalan, ya bayyana cewa:

"Wannan shirin ya sa na kulla huldodin dangantaka da mutane daga ko'ina a duniya. Idan na gama karatuna, ko kuma a lokacin hutu, zan iya ziyarar abokaina a kasashen ketare. A nan dai, ni ma ina gayyatar abokaina da a halin yanzu suke nan Bonn zuwa gidanmu a Kwalan, saboda babu nisa tsakanin biranen biyu. Ina nuna musu birnin. Wata rana, idan ni ma na ziyarci kasarsu, babu shakka, su ma za su karbe ni da hannu biyu-biyu. Hakan kuwa shi ne kulla zumunci tsakanin al'ummomi."

 • Kwanan wata 29.12.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvmr
 • Kwanan wata 29.12.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvmr