Shirin gudanar da zaɓe a Najeriya | Labarai | DW | 27.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin gudanar da zaɓe a Najeriya

Al'ummar Najeriya za su kada ƙuri'unsu a zabukan shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokokin ƙasar.

'Yan sanda na gadin katinan zabe gabanin zabukan Najeriya

'Yan sanda na gadin katinan zabe gabanin zabukan Najeriya

'Yan takara biyu ne dai ke kan gaba wajen neman shugabacin ƙasar da suka haɗa da shugaba mai ci yanzu Goodluck Jonathan da ke takara a ƙarƙashin jam'iyya mai mulki ta PDP da kuma tsohon shugaban mulkin sojan ƙasar a ƙarƙashin babbar jam'iyyar adawa ta APC Janar Muhammadu Buhari. Zaɓen wanda tun da fari aka shirya gudanar da shi a watan Fabarairun da ya gabata, an dage shi zuwa makwanni shida wanda ya kama Asabar 28 ga wannan wata na Maris da muke ciki bisa dalilai na tsaro.