1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Birtaniya na fita kungiyar EU ya kankama

Mohammad Nasiru Awal
March 29, 2017

A hukumance a wannan Laraba kasar Birtaniya ta mika takardar shirin ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai da za a dauki shekaru biyu ana tattaunawa kai.

https://p.dw.com/p/2aGI1
EU Großbritannien Brexit Brief Botschafter Barrow mit Tusk
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Herman

Kasar Birtaniyar dai wadda a bara al'ummarta suka kada kuri'ar amincewa da raba gari da Kungiyar Tarayyar Turai a wata kuri'ar raba gardama, a hukumance ta mika takardar shirin barin kungiyar mai shalkawata a birnin Brussels, inda aka mika takardar barin wannan kungiya ga Shugaban majalisar zartaswar EU Donald Tusk kamar yadda Firaminista Theresa May ta bayyana a gaban majalisar dokoki da ke birnin London.

Ta ce "Babban jakadan Birtaniya a Kungiyar EU a madadina ya mika matsayar gwamnatin Birtaniya abin da zai bijiro yarjejeniyar Kungiyar EU mai lamba 50. Lamarin da ke nuna cewa al'ummar Birtaniya sun daura damba ta aiwatar da aniyarsu ta barin Kungiyar ta EU."

Tim Barrow, jakadan Birtaniya a EU shi ya mika wannan takardar ta fara shirin fita daga EU wacce Firaminista Theresa May ta sanya wa hannu a kanta, ya kuma mikata ne ga Tusk a ofishinsa da ke birnin Brussels.

Rage tasirin ficewar Birtaniya daga EU

Brüssel Donald Tusk zu Brexit
Donald Tusk ya nuna wa manema labari takardar Birtaniya kan barin EUHoto: Reuters/Y. Herman

Bayan ya karbi takardar, Shugaban EU Donald Tusk ya ce kafin zuwa ranar Jumma'a zai gabatar wa sauran membobin kungiyar da shawara game da tattaunawar da za a yi. Da zarar an mika musu shawarar dole shugabannin EU din su gabatar da ka'idoji a taron kolin da za su yi ranar 29 ga watan Afrilu a Brussels. Daga baya wadannan ka'idojin za su kasance wani shirin doka a rubuce sannan a fara ainihin tattaunawa daga tsakiyar watan Mayu.

A cikin wata sanarwa da suka fitar a wannan Larabar shugabannin EU sun ce kungiyar za ta yi aiki a matsayin tsintsiya madaurinki daya kana za su kare muradunsu. Suka ce abinda za su ba wa fifiko da farko shi ne rage tasirin rashin tabbas da matakin da Birtaniyar ta dauka zai janyo wa al'ummominsu da harkar kasuwanci da kuma kasashe membobi.

Da ta ke maida nasu martani kan ficewar ta Birtaniya daga EU Ulrike Demmer mai magana da yawun Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce Birtaniya za ta ci gaba da kasancewa kawa ga kungiyar ta EU da ma Kungiyar tsaro ta NATO.