Shirin afuwa ga ′yan Kungiyar Boko Haram. | Siyasa | DW | 04.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin afuwa ga 'yan Kungiyar Boko Haram.

Gwamnatin Najeriya ta Sauko daga Kujerar nakin da ta hau a baya kan batun yafiya ga "yan Kungiyar Boko Haram, inda tace za ta duba yiwuwar yin hakan a yanzu.

Autor: Ubale Musa (Korr DW).in Abuja, Nigeria Below are the pictures of the arrival of the security meeting PIC FROM LEFT: CHIEF OF DEFENCE STAFF, ADMIRAL OLA IBRAHIM; CHIEF OF ARMY STAFF, LT.-GEN AZUBUIKE IHEJIRIKA AND CHIEF OF DEFENCE INTELLIGENCE, MAJOR-GEN. SANI AUDU ARRIVING FOR A MEETING AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON THURSDAY (4/3/13)

Sicherheitstreffen Nigeria

A Kokarin lalubo bakin zaren warware matsalar rashin tsaro data addabi Arewacin Tarayyar Najeriya, an gudanar da wani taron sirri tsakanin Shugaban Najeriyar Goodluck Ebele Jonathan da kuma Kungiyar Dattawan Arewa karkashin jagorancin tsohon Jakadan Najeriyar a Majalisar Dinkin Duniya Alhaji Bello Maitama Sule cikin daren Jiya Laraba yayin da kuma a Alhamis dinnan aka gudanar da wani taron sirri tsakanin manyan hafsoshin tsaron Tarrayar Najeriyar da shugaban kasar.

An dai ja daga kuma an raba gari a tsakanin kungiyar Jama'atu Ahalussunnah Lidda'awati Wal Jihad da akafi sani da Boko Haram da tai nasarar tada hankali da hargitsa lissafi a daukacin Arewacin Tarrayar Najeriyar da kuma Gwamantin Kasar da ta bisu cikin lungu da sako na Arewan tana farauta.

Kashim Shettima, Gouverneur von Borno State, Nigeria Usman Shehu, 15.06.2011, Maiduguri / Nigeria

Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno

Kokarin sulhu tsakanin bangarorin biyu ma dai ya kai ga turjiya ga Shugaban Kasar Goodluck Ebele Jonathan da a baya yace bashi da niyar yin afuwa ga "ya"yan Kungiyar da a cewar sa sun ki fitowa fili domin bayyana bukatun su.

To sai dai kuma taron Shugaba Goodluck da Dattawan Arewacin Kasar a karo na biyu, na shirin sauya akallar rikicin da yai sanadin asarar dubban rayuka cikin sama da shekaru ukun da suka gabata.

An dai kammala taron na sirri inda mahalarta taron ke cewa Fadar ta Aso -Rock ta sakko domin nazarin sababbin matakan da suka hada da yiwuwar yin afuwar, dake zaman sabon fata na sake tabbatar da zaman lafiya a daukacin yankin.

This image taken from video posted by Boko Haram sympathizers shows the leader of the radical Islamist sect Imam Abubakar Shekau made available Wednesday Jan. 10, 2012. The video of Imam Abubakar Shekau cements his leadership in the sect known as Boko Haram. Analysts and diplomats say the sect has fractured over time, with a splinter group responsible for the majority of the assassinations and bombings carried out in its name. (AP Photo) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL

Imam Abubakar Shekau, jagoran ƙungiyar Boko Haram

A cewar kakakin kungiyar Dattawan na Arewa Farfaesa Ango Abdullahi sun halarci wannan taronne bisa gayyatar Shuagaban Kasar.

A baya dai Gwamnatin kasar ta kira shi akai kasuwa game da yiwuwar warware rikicin da batun afuwar da a cewar mahukuntan Najeriyar ba ta yiwuwa ba tare da gane fuskokin masu bukatarta ba.

Abun kuma da ya kare tare da ta'azzara rikicin sannan da mai dashi na siyasa a tsakanin Arewacin kasar dake ganin matakin Gwamantin a matsayin wani yunkuri na rusa daukacin yankin, yayin da "yan uwansu dake kudu ke cewa babu bukatar haka din.

Siyasar kuma dake kara muni da jefa gwamantin kasar cikin halin tsaka mai wuya da kuma a cewar kakakin ta Labaran maku ba zai haifar da da mai ido ga makomar kasar ta Najeriya ba.

Sannu a hankali dai rikicin na tsallakawa ya zuwa su kansu Jamian tsaron da ake zargi da hannu wajen wasu jerin bama bamai dake tashi a Arewan wanda kuma ga dukkan alamu idon alummar kasar ke kara komawa kansu a yanzu haka.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar/US

Sauti da bidiyo akan labarin