Shirin Abu Namu(19.06.2019) | Zamantakewa | DW | 24.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shirin Abu Namu(19.06.2019)

Shirin na wannan mako ya yi nazari ne kan batun raba mukaman siyasa tsakanin maza da mata a Tarayyar Najeriya, inda matan ke kokawa da yadda suke tura mota ta bade su da kura ta tsere ta bar su.

Saurari sauti 09:39

Wannan matsalar ce ma ta sanya wasu kungiyoyin da ke rajin kare hakkin mata suka gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin Tarayyar Najeriyar da nufin nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda ba a bai wa matan kasonsu a bangaren mulki da gudanarwa da ma mukamai kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada. 

Matan dai sun gudanar da zanga-zangar ne da nufin ankarar da gwamnati bukatar ba su mukaman da suka cancanta da su musamman ma a yanzu da ake dakon nadin sababbin mukamai na ministoci da daraktoci da sauran mukaman gwamnati, bayan da aka sake rantsar da shugaban kasar Muhammadu Buhari a wa'adin mulkinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata.