1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Abu Namu

Lateefa Mustapha Ja'afar AAI
September 16, 2019

Shin ko kun san mene ne dalilin fargabar da matan kasar Afganistan ke yi a kan yarjejeniyar sulhun Afganistan da kasar Amirka? Ku biyo mu cikin shirin Abu Namu na wannan lokaci domin jin yadda lamarin yake.

https://p.dw.com/p/3Ph36

Shirin na wannan lokaci ya leka ne kasar Afghanistan, inda matan kasar ke nuna fargabar halin da za su iya kasancewa a nan gaba idan aka cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin Amirka da mayakan Taliban. Tattaunawar da ake gudanar da ita kusan tsawon shekara guda a Qatar, ana yin ta ne domin nemo hanyar da sojojin Amirka za su kammala ficewa daga kasar ta Afghansitan baki daya da kuma ajiye makamai a bangaren mayakan na Taliban. Bisa shiga tsakanin na Jamus, aka fara tattaunawa a tsakanin 'yan Afghansitan din domin lalubo mafita ga makomar kasar. A lokaci guda, matan kasar na fargabar cewa cimma yarjejeniya da 'yan Taliban ka iya salwantar da 'yancin da suka samu a baya-bayan nan.