Shinzo Abe ya sake lashe zaben Japan | Labarai | DW | 22.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shinzo Abe ya sake lashe zaben Japan

Miliyoyin al'ummar Japan dai sun fita zabe duk da ruwa da iska sai da suka dangana da tashoshin kada kuri'a don zaben 'yan takara 1,180 da ke neman kujera daga cikin kujeru 465 na majalisar.

Bayan nasara da ya samu ta tabbata, Shnzo Abe ya yi alkawarin daukar mataki mai karfi don ladabtar da kasar Koriya ta Arewa. Firaministan kasar ta Japan Shinzo Abe ya samu rinjaye cikin tsanaki a sakamakon zabe da ke fita, zaben 'yan majalisar dokoki da aka yi a wannan rana ta Lahadi, abin da zai ba shi dama ta kara tsayawa kai da fata wajen kalubalantar mahukuntan Koriya ta Arewa da ma kara himma wajen kare manufofin kasar da ke ta uku a fannin tattalin arziki a duniya.

Hadakar masu ra'ayin mazan jiyan da Abe ke jagoranta na kan hanyarsu ta samun  kujeru 311 daga cikin kujeru 465 na majalisar.

Miliyoyin al'ummar Japan dai sun fita zabe duk da ruwa da iska sai da suka dangana da tashoshin kada kuri'a don zaben 'yan takara 1,180 da ke neman kujera daga cikin kujeru  465 na majalisar.