Shin zuwa asibiti shi ne mafita ga cutar Basir, ko maganin gargajiya? | Amsoshin takardunku | DW | 02.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Shin zuwa asibiti shi ne mafita ga cutar Basir, ko maganin gargajiya?

Zuwa asibiti shi ne mafita ga cutar Basir, ba cushe-cushen magungunan gargajiya ba, wanda a karshe ana iya gamuwa da cutar 'Daji', wato 'Cancer'.

Soja Burger

Yawaita cin kayan ganye da kayan itatuwa suna taimakawa kwarai wajen maganin Basir.

A Likitance abinda ake kira Basir shine yanayi, da wasu abubuwa da kan taso da suka shafi wajen dubura. Ko wani abu na bullukowa a duburar mutum, ko jini yana zuba, ta irin wa'yannan fanni ko mataki daban-daban, shi ne za mu ce Basir, wanda kuma mutane suke ce masa a turance 'Pile', ko kuma a Likitance ace masa 'Hemorrhoids', tare da wadannan, akwai wadanda ake kira 'Anal Fissure'. Dangane da 'Pile', idan mutum ya je bayan-gida, sai yaji wani abu ya turu a duburarsa, in ya taba, wata kila ya koma da kanshi, to wannan shine kamar matakin farko. Sannan kuma mutum yana iya zuwa yin bayan-gida ya ga jini ya feso, ko kafin ya fara ko bayan ya gama bayan-gidan, shima wannan rukunin 'Pile' ne da ake kira 'Hemorrhoid' wato na zubar jini kenan. Zai iya kaiwa matsayin da zai fito ya makale yaki komawa, ya ta zafi sosai, shima wannan rukunin 'Pile', wanda shine za mu iya cewa shine Basir din. Zai iya yiwa kuma mutum yaje zai yi bayan-gida sai ya ji yana jin radadi sosai a duburarsa, yawanci kuma irin wannan mutum ya dade bai yi bayan-gida ba, sai yayi tauri, sai ya fito da kyar, to a irin nan akwai yiwuwar rauni ya samu, wanda shi ake cewa 'Anal Fissure', to wannan duk za a iya cewa Basir ne kai tsaye. Sannan akwai kuma wanda yake samun yara, wanda zaka ga duburarsu ta zazzago, da a turance ake kira 'Rectal Prolapse', wannan rauni ne a bakin abin da ke daure hanyar bakin dubura.

Fit und gesund Salat

Ire-iren kayan lambun da ke taimakawa masu matsalar cutar Basir kenan

Kuma zuwa asibiti shine mafita ga wannan cutar ta Basir, ba cushe-cushen magungunan gargajiya ba, wanda a karshe ana iya gamuwa da cutar 'Daji', wato 'Cancer'. Yana da kyau mutane su kauracewa cusa duk wani yamutsi da tarkace a ciki, mara kai bare basira. Duk yanayin da ya samu mutum, kamar daurewar ciki, ko yaji baya jin dadi, ko ya kasa bayan-gida,ko kuma yaji ya zauna ya dade a zaune, bayansa ya rike, wa'yannan duk ba Basir ba ne, zuwa asibiti ya kamata mutum yayi domin a duba shi, a bashi magani na asibiti. Duk wani yamutsi da kake ji, akwai wani dalili da zai kawo shi. Yawanci ma irin abincin da mutum yake ci ne, wani lokacin kuma wani abu ne ya faru a jikinka..

A Likitance, yawaita cin kayan ganye, da na itatuwa da kuma abincin da ba a cire sirfen ba, suna taimakawa jiki sosai har ma suyi maganin Basir din.