Shin wane ne Edward Snowden? | Amsoshin takardunku | DW | 01.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Shin wane ne Edward Snowden?

Fallasa bayyanan sirrin da Amirka da Birtaniya ke tatsa ya sanya Edward Snowden ya yi suna, amma kuma matashi ne mai basira sosai wanda ya yi karatu mai zurfi

A picture shows Edward Snowden in 2002 putting a clothespin on his chest for fellow employees when he worked as a webmaster and editor for a Japanese anime company run by friends in Maryland. REUTERS/as posted to katiebair.com by an online user in 2002, via Reuters (UNITED STATES - Tags: CRIME LAW POLITICS) NO SALES. NO ARCHIVES. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS

Edward Snowden

An haifi Edward Joseph Snowden, ranar 21 ga watan Yunin shekarar 1983, kuma shi tsohon ma'aikacin kwantiragi ne na hukumar tsaro ta Amirka wato NSA da kuma hukumar leƙen asiri ta CIA.

A watan da ya gabata ne ya yi suna domin falasa bayyanan sirrin da ya yi, waɗanda gwamnatocin Amirka da Birtaniya ke tatsa. kuma ya ce ya yi haka ne domin faɗakar da jama'a kan abubuwan da ake yi da sunansu domin su tantance mai kyau da mara kyau.

Jaridar The Guardian na Birtaniya ce ta fara wallafa waɗannan bayanai waɗanda suka yi ƙarin haske kan wasu shirye-shiryen sirrin da suka haɗa da ɗaukan bayanai daga wayoyin hannun mutanen da ke Turai da Amirka da kuma shirin nan na PRISM mai sarƙaƙiya wanda ke tatse bayanan duk wanda ke amfani da wata kafar sadarwa ta Internet.

Tun bayan wannan taɓargaza da aka yi, masu shigar da ƙarar Amirka suka zargi Snowden da satar kayayyakin gwamnati, da kuma bada bayyanan sirrin gwamnati ba bisa ƙa'ida ba, abin da masana tarihi suka ce shine mafi mahimmanci a tarihi domin, ya ƙarfafa shakkun da aka daɗe ana yi kan abin da mahukuntan Amirka ke yi da bayyanan al'umma

Iyali da farkon rayuwa

Snowden ya yi wayo ne a garin Wilmington da ke North Carolina. Mahaifinsa Lonnie Snowden mazaunin Pensylvania ne wanda shi soja ne a rundunar sojojin da ke kula da iyakokin ruwan Amirka, a yayinda mahaifiyarsa ta ke zaune a garin Baltimore da ke Maryland inda ta ke aiki a matsayin akawun kotun Tarayyar da ke Maryland.

Edward Snowden ya karanta Computer ne wani kwalejin al'umma mai suna Anne Arundel to sai dai saboda rashin lafiya da ƙyar ya kammala karatun. yayi aiki a sansanin sojin Amirka da ke Japan, inda ya koyi harshensu saboda sha'awar al'adunsu, ya kuma ce ya kan fahimci harshen Chinese kuma ya kan bayyana kansa a matsayin mabiyin addinin Buddha.

Yanayin aikinsa da zamantakewa da mutane

A shekarar 2004 ya shiga runduna ta musamman na dakarun Amirka domin samun horo, a lokacin ya ce yana so ya tafi yayi yaƙi a Iraƙi domin cika muradinsa na taimakawa wajen mutunta ɗan adam, to sai dai watanni hudu bayan nan an sallame shi saboda raunin da yayi a ƙafafunsa biyu wurin horaswar. Daga nan ne ya shiga hukumar leƙen asirin a matsayin ƙwarrare kan harkokin internet, inda daga nan a riƙa tura shi kasashe daban-daban.

A haƙiƙa ba mabuƙaci bane, mutun ne wanda albashinsa ta wadatar da shi sosai tunda kafin ya shiga wannan rikicin yana karɓar aƙalla dalan Amirka dubu 200 kowane wata.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba

Edita: Mouhamadou Awal Balarabe