1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

271008 USA McCain

Borchers, Jens / Washington (HR)October 27, 2008

Dukkan binciken jin ra´ayin jama´a da aka gudanar yanzu gabanin zaɓen shugaban Amirka, ɗan takarar jam´iyar Democrats Barack Obama ke gaban abokin hamaiyarsa ɗan jam´iyar Republicans John McCain.

https://p.dw.com/p/Fhht
John McCain da matarsa Cindy McCainHoto: AP

Yanzu haka dai ɗan takarar jam´iyar Democrats Barack Obama na gaban abokin hamaiyarsa ɗan jam´iyar Republicans John McCain da kimanin kashi 10 cikin 100. A jihohi masu muhimmanci mai jam´iyar ta Democrats ce ke kan gaba. Ko shin binciken jin ra´ayin jama´ar na ba da gaskiyar halin da ake ciki? Masu yaƙin neman zaɓen McCain dai ba su yarda da wannan ƙuri´a ta jin ra´ayin masu zaɓe ba saboda haka a cikin kwanakin da suka saura gabanin zaɓen sun mayar da hankali kan batutuwa guda biyu wato haraji da kuma ƙwarewarsu ta siyasa.

Ba bu tabbas ko John McCain zai iya angiza kan shi ko magoya bayansa da mataimakansa.

"Ni Baamirke ne ɗan gwagwarmaya. Kar ku saduda kuna ƙwarin guiwa, ku ci-gaba da gwagwarmaya." McCain kenan ya na ƙoƙarin ƙarfafawa magoya bayansa guiwa.

A kwanakin ƙarshen nan gabanin zaɓen McCain ba ya nuna gajiyawa inda a yaƙin neman zaɓensa yake mayar da hankali kan batutuwa biyu da yake fata za su ba shi galaba akan abokin hamaiyarsa na jam´iyar Democrats.

Ya ce: "Ƙara kuɗin haraji mai yawa ba shi ne mafita daga mawuyacin halin tabarbarewar tattalin arziki ba. Amma abin da zai faru kenan idan Democrat ta karɓi ragamar mulki a Washington. Bai kamata mu kyale haka ya faru ba."

Yanzu haka dai ana dai cece-kuce mai tsanani yayin da aka shiga zagaye na ƙarshe a yaƙin neman zaɓen. Duk da cewa alƙalumman da masana da kuma Barack Obama suka bayar sun yi nuni da cewa jam´iyar Democrats za ta rage haraji ga kashi 95 cikin 100 na Amirka masu matsakaicin ƙarfi, amma McCain na yi ta kwatanta ´yan adawarsa da waɗanda za su ƙarawa jama´a nauyi na haraji.

Da yawa daga cikin masu tsara dubarun yaƙin neman zaɓen jam´iyar Republicans sun ce wannan ita ce damar da ta ragewa McCain wato sanya tababa a zukatan masu zaɓe musamman a jihohin da Obama ya yi masa fatankau. McCain ya haƙiƙance cewa Obama bai dace ya shiga fadar white House ba, domin ba ya da ƙwarewa wajen tinkarar matsaloli na ƙasa da ƙasa.

Ya ce: "Sineta Obama ba zai iya mayar da martani da ya dace ga irin waɗannan mastaloli ba. Dukkan mu san da haka kuma mun shaida irin kurakuran da ya ke tabƙawa."

McCain ya yi amfani da hasashen da mataimakin Obama, Joe Biden yayi ba da shiri ba. Inda ya ce a cikin watannin shidan farko na shugabancin Obama za a iya fuskantar wani rikici a duniya domin jarraba sabon shugaban, wato kamar rikicin ƙasar Kuba da ya zama zakaran gwajin dafin John F. Kennedy.

An jiyo tsohon sakataren tsaro a gwamnatin Reagan wato Gaffney na kashedin cewa idan ɗan takara ya nuna cewa bai da niyar amfani da ƙarfin soji ko ba da hurumin yin haka to wannan wata alama ce ta gazawa.

Ƙaruwar barazana daga ƙetare da rashin tsaro da kuma ƙarin kuɗin haraji abubuwa ne dake ƙara saka Amirkawa cikin halin rashin sanin tabbas. McCain ya yi nuni da cewa wannan barazanar za ta tabbata idan Obama ya lashe wannan zaɓe.