Shin Jamuasawa zasu yi maraba da baki a gasar cin kofin duniya?
April 22, 2006Mummunan harin da aka kaiwa wani bakar fata a gabashin Jamus ya tada wata muhawwara a tsakanin al´umar wannan kasa game da ko a shirye Jamusawa suke su karbi bakwancin duniya baki daya a gasar cin kofin duniya da za´a yi a kasar a lokacin bazara. Tambayar da kowa ke yi ita ce ko al´umar wanan kasa zasu amince da taken wanan wasa wanda ke yiwa duniya maraba da zuwa gidan abokai. Firimiyan jihar Bavaria mai ra´ayin mazan jiya, Edmund Stoiber ya kasance fitattacen dan siyasar kasar ta Jamus ya shiga jerin masu yin kira da a dauki sahihan matakai inda yayi kira ga hukumomin kasar da su haramta dukkan ayyuka irin na kyamar baki a filayen wasan kwallon kafa. A yau asabar dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar yin Allh wadai da ayyukan masu matsanacin ra´ayin kyamar baki a garin Halberstadt dake gabashin Jamus. Ana kara nuna damuwa game da karuwar ayyukan ´yan ra´ayin kyamar baki bayan harin da aka kaiwa bakar fatar dan asalin Habasha. har yanzu dai yana kwance rai hannun Allah.