1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin Afrika za ta iya wadata Jamus da makamashin gas?

Zainab Mohammed Abubakar
August 12, 2022

Jaridun Jamus sun yi tsokaci tare da sharhi akan shirin samar da makamashin gas daga Afirka zuwa Turai domin maye gurbin makamashin daga Rasha

https://p.dw.com/p/4FTY0
Mosambik | Provinz Inhambane | Sasol Erdgasexploration
Hoto: Roberto Paquete/DW

Jaridar Die Welt ta buga sharhi mai taken "Shin Afrika za ta iya ceto Jamus ta wadata da makamashin iskar gas"?. Jaridar ta ce Senegal na da albarkatu masu yawa, kuma Jamus tana sha'awar su sosai. Amma shirin shugaban gwammnati Olaf Scholz na fuskantar adawa.

Senegal na da manyan tsare-tsare

Mosambik | Provinz Inhambane | Sasol Erdgasexploration
Hoto: Roberto Paquete/DW

Kasar ta Afirka ta Yamma na son yin amfani da sabon gibin da aka samu na samar da iskar gas ta wadata kasashe masu ci gaban masana'antu irin su Jamus da iskar gas nan gaba. Tuni dai aka fara aikin hakar albarkatun iskar gas, inda sama da kubik mita biliyan 425 na iskar gas ke jiran hakowa a gabar tekun Senegal da Mauritania, a cewar alkalumman kamfanin makamashi na BP. 

Duk da cewa kasar na da tarin albarkatun iskar gas, yakin Ukraine da kuma matakin Rasha na janye gas dinta ne suka sanya fatan samun wannan bunkasa. Sai dai aikin mai sarkakiya ne kuma Senegal na iya fitar da iskar gas zuwa kasashen waje ne kawai akalla daga karshen shekarar 2023 zuwa gaba.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung sharhi ta yi mai taken "Afirka ta samu karin tsawon rayuwa da shekaru goma, babu wata nahiya da ta sami karuwa mafi girma tun shekara ta 2000".

 

A 'yan kwanakin nan babu karancin labarai mara dadi daga Afirka.

 

Ghana | Strassenverkehr in Kumasi
Hoto: Thomas Imo/photothek/picture alliance

Kama daga yaki a Habash da yunwa a Madagascar sai ta'addanci a yankin Sahel da matsalar bashi zuwa tabarbarewar tattalin arziki. 

Ana dai kokarin nunar da cewar halin da ake ciki a nahiyar ya yi muni sosai, ko da idan an kwatanta da yanayin da duniya ta tsinci kanta a ciki. Sai dai a wasu lokuta ana manta ambaton cewa Afirka na samun ci gaba cikin nasara a wasu bangarorin.

Ana iya ganin hakan a wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta wallafa a makon jiya. Bisa ga binciken, matsakaicin tsawon rayuwa a Afirka ya karu da kusan shekaru goma tun daga 2000, fiye da kowane yanki na duniya. WHO ta yi amfani da abin da ake kira "tsawon rai mai lafiya" a matsayin kima, watau matsakaicin adadin shekarun rayuwa da za a sa rai lokacin haihuwa.

Hukumar ta danganta wannan cigaba mai dadin ji, da cewar a yanzu mafi yawa daga cikin 'yan Afirka na samun damar zuwa wuraren kula da lafiyarsu, in ji daraktanta na yankin, Matshidiso Moeti yayin gabatar da rahoton.

 

Sakataren harkokin wajen Amurka na kokarin dakile tasirin Rasha

Südafrika Präsident Cyril Ramaphosa und Blinken
Hoto: Andrew Harnik/AFP

Wannan shi ne taken sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa game da ziyarar da ministan harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai a wasu kasashen Afirka a wannan makon mai karewa.

Jaridar ta ce Blinken ya fara yada da zango ne a Afirka ta Kudu inda ya samu kyakkyawar tarba daga takwararsa ta kasar Naledi Pandor a birnin Pretoria kafin ya shige Rwanda da Kongo. 

Ana dai ganin kamar Afirka na goyon bayan Rasha, duba da yadda suka kaurace wa kuri'ar Allah wadai da mamayen da ta yi wa Ukraine a zauren Majalisar Dinkin Duniya. 

Manazarta dai na ganin cewar ko ziyarar ministan harkokin wajen Amurkan ba zai canja komai ba game da yadda al'ummar Afirka ta kudu ke martaba Rasha, duba da goyon bayan tarayyar Soviet ga yaki da wariyar launin fata na Apatheid.