Shimon Peres na kwance a asibiti | Labarai | DW | 14.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shimon Peres na kwance a asibiti

Tsohon shugaban kasar ta Isra'ila a yanzu haka jikinsa ya shanye kuma baya iya numfashi da kansa don haka komai sai abinda na'ura ta yi abin da ke nuna tsananin jin jiki da yake yi.

A cewar kakakin tsahon shugaban, Shimon Peres haka kwazam a jiya Talata ya kamu da mummunar cutar. " Shugaba na tara a jerin shugabannin Isra'ila ya kamu da mummunan shanyewar jiki, kuma hakan ya hadu da fashewar jijiyoyi a inda jini ke ta fita. Kwararrun likitoci dai na can na iya abinda za su iya don ceto ransa. A yanzu Shimon Peres sai ta na'ura yake numfashi" Ofishin tsohon shugaban ya bada sanarwa a safiyar yau Laraba cewa lamarin yana da muni, amma dai ana kokarin shawo kansa.