Shigar da yara kanana aikin Soji | Zamantakewa | DW | 13.12.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shigar da yara kanana aikin Soji

Kungiyar Human Right Watch na yaki da tilasta yara aikin soji

default

Yara a filin daga

Dokar kasar Tschadi dakeyankin tsakiyar Afrika,kamar sauran kasashe ta tanadar dacewar dole ne mutum yakai shekaru 18,kafin ya shiga aikin soji a hukuman ce.Sai dai sakamakon cigaban tasheshen hankula da kasar ta gada saboda juyin mulki a tarihinta kusan shekaru 50 bayan samun ‚yancin kai daga mulkin mallaka.Inda a kullum Iyaye ke kokawa dangane da yadda yaransu ke tserewa daga gida suna hadewa walau da dakarun gwamnati ko kuma na ‚yan tawaye kamar yadda Aisha Kili ,mai shekaru 38 da haihuwa ta bayyana yadda ɗanta mai shekaru 14 ya hade da dakarun tawaye na FUC dake fada a gabashin Tschadi……

„ƊAna ya haɗe da da dakarun adawa alokacin da yake kimanin shekaru 14 da haihuwa.Wata rana ya tafi makaranta,har lokacin tashi yayi ban ganshi ba.A daren baki ɗaya banyi barci ba,saboda na kwana da tunani da zulumi adangane da inda zai yi barci.,da kuma inda zai samu abincin da zai ci.Daga baya ma na fara tunanin shin ko an kashe shi ne akan hanyar komowa daga makaranta?Wayewar gari keda wuya sai na tura ‚yar uwarsa nemanshi a dukkannin gidajen abokanan sa ,inda nan aka faɗa mata cewar ya hade da dakarun tawaye dashi da abokin sa guda.Bai komo gida ba sai bayan yakin Guereda daya kare a ranar 1 ga watan Disamban 2006“.

Abun mamaki shine wannan yaro ɗan shekaru 14 da haihuwa ya komo gida yana alfaharin cewar shi a yanzu Namiji ne.Da mahaifiyarsa ta tambaye shi dalilin zuwansa filin daga sai ya kada baki yace,an kashe dukkannin iyali na shi yasa ni ma na tafi yaki.Mahaifiyarsa ta tambayeshi kos hin wannan bindiga daya dawo dashi bashi da nauyin ɗauka?budar bakin yaron sai yace bashi da nauyi.Daga wannan rana daya fice bai sake komowa gida ba,saboda abunda ya danganta da yawan suratan mahaifiyar tasa.

Alokacinda kungiyar kare hakkin jama’a ta human right watch tayi hira da Aisha a watan maris na shekarata 2007 da muke ciki,tana cike da fatan cewar wata rana ɗanta zai ajiye bindiga ya komo gida,musamman bayan cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin ‚yan tawayen Tchadi da gwamnatin kasar.Sai dai murnar ta ya koma ciki domin wannan yarjejeniya da aka cimma na zaman lafiya bai tabbatar da tsaro a fadin kasar ta tchadi ba.Adangane da hakane Aisha a watan janairu ta aiki ɗan ta mai shekaru 20 da haihuwa ,domin karɓo ƙaninsa daga kungiyar ‚yan tawayen ta FUC,amma maimakon komowa da ɗan uwan nasa,sai shima Wan ya haɗe da wannan ƙungiya.Inda akan hakane Aisha ta bayyana tsoron ta na asaran ‚yayan nata biyu…

„Ina ganin cewar na rasa Yara na duka biyu wa waɗannan mayaka na tawaye,dake kwaɗayin amfani da kananan yara wajen cimma bukatunsu,wanda ba yara mazan kaɗai suke amfani dasu ba har da ‚yan mata.Sai dai ina fatan wata rana zan sake ganin Yara na dukkanin su biyu.

A yanzu hakan dai dakarun soji na gwamnatin Tchadi na kokarin ganin cewa sun murkushe mayakan tawayen dake cigaba da tayar da hankula musamman a yankin gabashin wannan kasa.Rahotanni sun tabbatar dacewar a faɗan daya gudana tsakanin ɓangarorin biyu a shekara ta 2006,dukkannin ɓangarorin biyu sunyi mafani da yara kanana a matsayin sojojin zuwa filin daga.Anyi amfani da yara da shekarun su ya kama daga 8 zuwa sama amatsayin mayaka,ko masu tsaro ko masu yin girki,ko kuma a matsayin masu zuwa duban ta inda za’a kawo hari wa abokan faɗa.

Sai dai wannan hali da yaran suka kasance ya zame wani nau i ne na zalunci inji wani manazarcin harkokin kasar ta Tschadi dake birnin Njamena,Alh Yusuf Mohammad Saleh…..

A yankin gabashin Tschadin alal misali,wannan fada yakan hadar dana kabilanci,inda yara da kann gudu saboda tserewa da rayukansu,ko kuma neman mafaka kann faɗa kai tsaye cikin hannayen waɗannan mayunwatan kungiyoyi dake neman sojoji ta kowa ne hali,kamar su FUC dake da sansanin su a garin Dar Tama.

To bayan waɗannan kungiyoyin sun gama amfani tare da cin moriyar waɗannan yara nedai,sukan yi watsi dasu,ba tare da biya musu bukatu ko cikanta alkawuran da suka daukar musu da suka hadar da na kudi ,wanda dalili kenan dake kwaɗaitar wa yaran.kamar yadda Yusuf Saleh ya yi bayani…

Tun daga watan mayu wannan shekara ta 2007 nedai gwamnatin Tchadi tare da da kungiyar yan tawayen ta FUC,suke bawa kungiyar kula da rayuwar yara ta Majalisar Ɗunkin Duniya ta UNICEF,haɗin kai adangane da gano waɗannan kananan yara da ake amfani dasu wajen faɗa,tare da sake haɗe su a alumma ko kuma sanya waɗanda shekarun su suka kai na shiga soji,cikin ayayrin dakarun gwamnati.To sai aKungiyar kare hakkin Jama’a ta Human Right Watch na bayyana shakku dangane da ɗorewan wannan shiri a ɓangaren ita gwamnatin tchadin,da ma sahihancin sa.

Faransa dai ta na jagorancin ƙasashen duniya dake cigaba da matsin lamba wa gwamnatin tchadin wajen kwance ɗamarar yakin kananan yara dake aikin sojin,sai dai kokarin ta ita kadai bazai tasirin da ake bukata ba,har sai kasashen dake da dangantakar soji da harkokin makamai da tschadin,da suka haɗar da Amurka sun bada hadin kai wajen ganin cewar an ceto wa waɗannan yara rayuwarsu.,kamr yadda kungiyoyin kare hakki jamaa na kasa da kasa ke kokarin yi.

To sai dai mafi yawa daga cikin waɗannan yaran na ganin cewar basu da wata rayuwa data shige wannan da suke ciki ta faɗa,tunda mafi yawa daga cikin Iyalansu sun rasa raayukansu ta wannan hanya kamar yadda wani Dottijo mai shekaru 62 da haihuwadake Garin Barra ya fadawa ,kungiyar human Right Watch.

„Ɗana mai shekaru 15 da haihuwa da ‚yayan Yayyuna guda uku waɗanda shekarunsu yake 12,da 15 da 16,sun haɗe da mayakan FUC,amma hakan bai bani tsoro ba,tunda wannan shine zaɓinsu.Domin Ɗana yana kokari sosai a makaranta ,banji daɗi ba daya watsar da karatu ya haɗe da ‚yan tawaye domin faɗa,amma bani da tacewa“

Haka dai Iyaye da dama ke juyayain irin wannan haɗari da yaransu kann faɗa,walau cikin sani ko kuma ta hanyar tilas.

Abun Fadi dai anan shine yara a ko ina suke sune shugabannin Gobe,don haka hakki ya rataya akan kowane Bangare na tallafawa waɗannan yara zaɓin makoma ta gari.

 • Kwanan wata 13.12.2007
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CbOo
 • Kwanan wata 13.12.2007
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CbOo