Shekau ya sake fitowa | Labarai | DW | 07.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekau ya sake fitowa

Jagoran daya bangaren kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ce babu guda bau ja da baya a aikinsu na kai hare-hare, duk kuwa da ikirarin nasara da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da yi.

A Najeriya, shugaban daya bangaren kungiyar mayakan tarzoma ta Boko Haram Abubakar Shekau ya yi alkawarin ci gaba da kai hare-hare, duk kuwa da ikirarin samu nasara da gwamnatin kasar ke yi kan murkushe su daga tushe. Cikin wani sako na faifan bidiyon da ya sako a ranar Talata, Shekau ya ce suna nan a kan fafutukarsu ta wargaza tsarin rayuwa ta turawan yamma da mutane suka runguma.

Dakarun Najeriyar dai na ci gaba da gumurzu tare da motsa dajin Sambisa, wato maboyar mayakan na tarzoma.

Sai dai masu sharhi sun ce akwai alamun gajiyawa tare da Abubakar Shekau a sabon bidiyon, amma suna jaddada cewa hakan ba alamu ne na karshen ayyukan na ta'adda ba. A share guda kuwa, Najeriya da sauran kasashe makobta na cewa ne suna kan matsayinsu na ganin bayan ayyukan wannan kungiya.