Shekaru 56 da samun ′yanci a Nijar | Labarai | DW | 03.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekaru 56 da samun 'yanci a Nijar

Mahukunta a Nijar sun ce duk da matsalar tsaro da ma na sauyin yanayi cikin shekaru biyar kasar ta samu nasara wajen rage talauci.

Niger Mahamadou Issoufou Präsidentschaftswahlen

Shugaba Mahamadou Issoufou

Shugaban Jamhuriyar Nijar ya sake bada karfin gwiwa ga al'ummar yankin Diffa da ke a Kudu maso Gabashin kasar a bisa cewa gwamnatin kasar za ta murkushe ayyukan 'yan ta'adda a wannan kasa da Boko Haram ta gallabi yankin, inda shugaban ya bukaci al'umma su mara wa gwamnati baya a kokarin da take yi na aiwatar da ayyuka na cigaba. Shugaba Mahamadou Issoufou ya bayyana haka ne a wani jawabi ta kafar talabijin na kasa yammacin jiya Talata wayewar gari yau Laraba da ke zama ranar da kasar ke cika shekaru 56 da samun 'yancin kai daga kasar Faransa.

Shugaba Issoufou da ya samu damar yin tazarce bayan nasara a zaben watan Maris ya ce dakarun sojan hadin gwiwa na kasashe da ke makwabtaka da Nijar na kokari na ganin bayan kungiyar 'yan ta'addar na Boko Haram da ke da sansani a Najeriya.

Shugaban ya ce duk da matsalar tsaro da ma na sauyin yanayi cikin shekaru biyar kasar ta samu nasara wajen rage talauci tsakanin al'umma, sannan ta samu ci gaba a fannin bunkasar tattalin arziki da kashi shida cikin dari.