Muhammad Tanko a hagu da Murjanatu Katsina a tsakiya na daga cikin ma'aikatan sashen Hausa na farko. Wannan hoton dai an dauke shi ne a ranar 3 ga watan Mayu shekara ta 1972, a birnin Kolon.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Malamai a bakin aiki
Tun bude sashen Hausa, ma'aikatansa sun kasance masu maida himma don gabatar da shirye-shirye masu kayatarwa. Hakan kuwa na samuwa ne idan an shirya da kyau tun farko.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Karanta labarai
Daga cikin shirye-shiryenmu tun farkon bude tashar, labaran duniya da na Afirka da kuma rahotanni kan al'amuran yau da kullum, sun kasance muhimman batutuwan da muke mayar da hankali kansu.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Hadin kan ma'aikata
Tsaye a baya (hagu zuwa dama) Gerhard Manstein, Bello Sani, Winfried Bergmann, Mahmud Imam, Samuel Musa, Malama Degener da Kabo Idris. A gaba: Murjanatu Katsina, Wolfgang Teuscher (shugaban sashe), von Tiesenhausen da Benji Metide (3.5.1972).
Shekaru 55 na sashen Hausa
Shawara kan shirye-shirye
A wannan hoto ana iya ganin: Hans Dieter Klee da Edda Görke da Muhammad Tanko suna tattaunawa kan shirye-shiryen sashen Hausa.
Shekaru 55 na sashen Hausa
A ci duniya da tsinke
Labarai da shakatawa daga Sashen Hausa.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Shugaba da ma'aikatansa
A wannan hoto ana iya ganin: Edda Görke, Muhammad Tanko, Walter Priebe(shugaban sashen Hausa), sai kuma Murjantu Katsina (3.5.1972).
Shekaru 55 na sashen Hausa
Ra'ayin malamai
Daga hagu zuwa dama: Ado Gwadabe (daga baya ya zama shugaban sashen Hausa), Yahaya Musa, Ibrahim Maccido, Sani Dauda a cikin shirin ra'ayin malamai, shirin da har yanzu muke gabatarwa a ranakun Asabar da Lahadi da yamma. Wannan hoton an dauke shi ne a ranar 3 ga watan Mayu shekara ta 1972.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Abokan aiki na hakika
(A tsaye): Gerhard Manstein, Ado Gwadabe, Dauda Abari, Kabo Idris, Luis Mertens, Edda Görke, Bello Mahmud, Muhammad Tanko, Alhaji Katsina. A zaune akwai Malama Metide, Walter Priebe da Ibrahim Maccido.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Shekaru 15 na sashen Hausa
Sashen Hausa na DW ya cika shekaru 15 a shekarar 1978. Masu taya shi biki a wannan hoto su ne (daga hagu zuwa dama): Ado Gwadabe, Ali Ramadan (na sashen Suwahili), Monzlinger (dauke da faranti), Othman Miraji (na sashen Suwahili), Nazmun Nesa (daga sashen Bengali), Sabo Ahmed, Walter Steigner (Darekta-Janar), Umaru Aliyu.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Gerhard Manstein
Gerhard Manstein yana daya daga cikin editocin farko da suka yi aiki a sashen Hausa na DW a shekara ta 1963, kafin daga baya yayi aiki a fannoni dabam-dabam a DW har zuwa shekara ta 2002.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Shirin ilimantarwa na Ji ka karu
Ji Ka Karu, shiri ne na musamman domin ilimantar da yara matasa da ke nahiyar Afirka ta rediyo da yanar gizo da kuma wayar salula. Manufar wannan shiri ita ce ilimantar da matasa ta hanyar nishadi, domin karfafa musu gwiwa wajen tunanin rayuwarsu da ba wa kansu shawara a kan abubuwan da suka ji.
Shekaru 55 na sashen Hausa
LbE a bakin aiki
Masu shirya wasan kwaikwayo na shirin Ji Ka Karu a bakin aiki a Abuja, Najeriya.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Ma'aikatan sashen Hausa a 2005
Daga hagu: Abba Bashir, Thomas Mösch, Ahmad Tijani Lawal, Zainab Mohammed Abubakar, Yahaya Ahmed, Hauwa Abubakar Ajeje, Ibrahim Sani, Umaru Aliyu, Yahouza Sadisou Madobi, Abdullahi Tanko Bala.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Bankwana da aiki
Bayan shekaru 40 na aiki a sashen Hausa, a shekarar 2008 Edda Görke ta yi ritaya daga aiki. A wannan hoton Edda Görke wadda a sashen Hausa aka fi saninta da suna Malama, tana jawabin godiya bayan ta karbi kyautar bankwana daga shugaban sashen Hausa Thomas Mösch. Bikin ritayarta ya zo daidai da bikin cikar sashen Hausa na DW shekaru 45 da kafuwa.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Babban bako a Kano
Tsohon shugaban tashar Deutsche Welle Erik Bettermann da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, a shekarar 2008 lokacin da babbar tawagar Deutsche Welle ta kai ziyarar ban-girma a fadar Sarkin na Kano.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Karfafa dangantaka
Babbar tawagar DW a lokacin ziyara Freedom Radio da ke Kano a 2008. A lokacin an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin DW da Freedom Radio. Tashar daya ce daga cikin tashoshi kawayen DW a kasashen Afirka. Sabanin Nijar, a Najeriya doka ta hana tashoshin cikin gida watsa shirye-shiryen ketare kai tsaye.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Tashoshi kawayen DW a Nijar
Radio Anfani na daya daga cikin tashohi kawayen DW da ke watsa shirye-shiryenmu kai tsaye ta FM a Nijar. A wannan hoton da aka dauka a cikin watan Fabrairun shekarar 2013ana iya ganin, daga dama: Gazali Abdou, Thomas Mösch, Boucar Gremah (Darakan Radio Anfani), Mahaman Kanta.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Wakilanmu a ko'ina a kullum
Don kawo muku sahihan rahotanni da labarai masu inganci, wakilan DW suna kowane sako da lungu na duniya. Wadannan wakilai suna aiki ba dare ba rana, a wasu lokutan ma cikin hadari, don samo rahotanni da labarai, kamar a wannan hoton wakilinmu na yankin Niger Delta Muhammed Bello.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Ma'aikatan sashen Hausa a 2011
A baya (daga hagu); Ahmad Tijani Lawal, Mouhamadou Awal, Saleh Umar Saleh, Mohammad Nasiru Awal, Fatihu Sabi'u, Yahouza Sadissou, Fouad El-Auwad, Umaru Aliyu, Thomas Mösch. A gaba (daga hagu); Abdourahmane Hassane, Pinado Abdu, Sussane Bergers-Rose, Zainab Mohammed, Abdullahi Tanko Bala, Usman Shehu Usman, Halima Balaraba Abbas.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Gasar kaci-kaci don karfafa hulda
A dangane da gasar cin kofin kwallon kafar duniya da Jamus ta karbi bakoncinsa a 2006, DW ta bukaci masu sauraronta da masu amfani da shafukanta na intanet su yi zanen yadda suke ganin Jamus. Liman Mahdi Gashua, Najeriya, mai sauraron sashen Hausa na DW ya ci kyauta ta wanda ya zo matsayi na biyu da wannan zanen.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Ma'aikatan sashen Hausa a 2013
Daga hagu zuwa dama: Halimatu Abbas, Suleiman Babayo, Mouhamadou Awal, Susanne Bergers-Rose, Saleh Umar Saleh, Youssoufou Abdoulaye, Umaru Aliyu, Zainab Mohammed, Ahmed Salisu, Usman Shehu Shehu, Lateefa Mustapha, Thomas Mösch, Fatihu Sabi'u, Pinado Abdu-Waba, Mohammad Nasiru Awal, Yahouza Sadissou, Britta Grüner
Shekaru 55 na sashen Hausa
Sharhin Bundesliga Kai Tsaye
Tun daga kakar wasanni ta 2016/2017 sashen Hausa ya fara gabatar da sharhin wasannin lig-lig na Jamus wato Bundesliga kai tsaye ta akwatunan rediyo. A kowane mako ma'aikatanmu na gabatar da karawa daya mafi daukar hankali daga cikin wasannin na Bundesliga. Mu kan gaiyaci kwararru daga tashoshi kawayenmu don sharhi kan wasannin. Muna kuma ba wa masu binmu ta Facebook damar tofa albarkacin bakinsu.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Bankwana da gwarzon wasanni
A cikin watan Oktoban shekara ta 2016 Malam Umaru Aliyu ya yi ritaya bayan ya shafe shekaru 41 yana aiki a sashen Hausa na DW. Bayan jagorantar tsohon shirinmu na "Duniya Ina Labari" Umaru Aliyu ya kasance jagoran shirin "Labarin Wasanni". Muryarsa ta kasance tambari na sashen Hausa. Yana daya daga cikin wadanda suka fara gabatar da shirin Bundesliga Radio Kai Tsaye.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Karfafa hulda da masu sauraro
Shugaban sashen Hausa Thomas Mösch lokacin mika kyautar rigar Jersey ta Bayern Munich ga Bala Muhammad Dambam a Bauchi, wanda ya yi nasara a gasar zaban matashin da ya aka fi kauna a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa da ke wasan Bundesliga a Jamus. A tsakiya Jummai Liman Bello ta gidan rediyon Bauchi, daya daga cikin tashoshin da ke hulda da DW-Hausa.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Hangen Dala....
A 2017 sashen Hausa ya gabatar da mahawarori kan bakin haure mai taken "Hangen Dala ba Shiga Birnin ba". An yi a Yamai, Nijar da Jos, Nijeriya. A hoton lokacin mahawarar a Jos, daga hagu: Aliyu Tilde dan kare hakin dan Adam, Jummai Isandu Madaki 'yar kare hakin mata da yara, Rabiu Abdullahi, tashar Unity FM Jos, Usman Shehu, DW Bonn, Solomon Dalong ministan matasa da wasanni na Najeriya.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Damar fadin albarkacin baki
An ba wa jama'a da suka halarci zauren mahawarar damar bayyana ra'ayinsu kan matsalar ta bakin haure da yadda suke ganin za a magance ta. Nan dai wani matashi ne Muhammad Al-Hassan daga Jos yana bayyana ra'ayinsa.
Shekaru 55 na sashen Hausa
Ma'aikatan sashen Hausa a 2017
Daga hagu zuwa dama. Britta Grüner, Lateefa M. Ja'afar, Ramatu Garba, Aliyu M. Waziri, Mohammad N. Awal, Yusuf Bala, Abdourahamane Hassane, Thomas Mösch, Muntaqa Ahiwa, Zainab Mohammed, Gazali Abdou, Aliyu Abdullahi, Usman Shehu, Ahmed Salisu, Abdul-raheem Hassan, Mouhamadou Awal, Suleiman Babayo, Batoul Kidadi, Shamsiyya Hamza, Salissou Boukari