Shekaru 50 da yin juyin mulki a Najeriya | Siyasa | DW | 15.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 50 da yin juyin mulki a Najeriya

Kama daga sojan kasar da ke tsakiyar rikicin ya zuwa 'yan siyasar da ke tunanin an bata dama ragowar talakawan da rayuwarsu ta sauya dai, ranar 15 ga watan Janairu na da muhimmanci ga kowa.

Firaministan Najeriya Abubakar Tafawa

Firaministan Najeriya Abubakar Tafawa

A ranar ta 15 ga watan Janairun shekara ta 1970 ce dai sojan kasar suka karbi sarandar 'yan tawayen neman tabbatar da Jamhuriyar Biafara, to sai dai kuma mafi tasiri a siyasa na zaman juyin mulkin shekara ta 1966, da ya kai karshen demokaradiyar farko sannan kuma ya shigar da tsarin mulkin soja cikin kasar. Ana dai kuma kallon juyin mulkin a matsayin danbar rikici na kabilanci da ma yakin basasar kasar na shekaru biyu da rabi. Ra'ayi cikin kasar dai ya rabu a tsakanin masu tunanin juyin mulkin ya dace da mafi yawansu ke zaman al'ummar Kudu maso Gabas da kuma masu adawa da hakan daga ragowar sassan Arewacin kasar da Kudu maso Yamma.

Shugaban Najeriya a yayin juyin mulkin Nnamdi Azikiwe

Shugaban Najeriya a yayin juyin mulkin Nnamdi Azikiwe

Cin hanci ne sanadin kifar da gwamnati

Kama daga Kaduna inda 'yan juyin su kai nasarar hallaka Sardauna kuma shugaba ga gwamnatin ta Arewa, ya zuwa birni Legas inda a can ma Abubakar Tafawa Balewan da ke shugabantar gwamnatin Tsakiya ya yi asarar ransa, babbar hujjar sojojin dai na zaman cin hanci da karbar na goro a bangare na masu siyasar.

To sai dai kuma shekaru 50 bayan juyin a fadar Mallam Adamu Chiroma da ke zaman tsohon ma'aikaci a ofishin Sardaunan na Kaduna, bai san da batun hancin ba balle neman na goro a bangare na masu siyasar.

Kokarin korar kare a gindin dinya ko kuma kokari na gyara na kasa, duk da banbanci da ma kila rigingimu na siyasar da ake yi wa kallon sun zamo ado a Jamhuiyar farkon dai, an fito daga rikicin juyin mulkin da ma yakin basasar da ya haifar tare da hadewar ra'ayin cewar sojan kasar ta Najeriya sun yi kuren da yai rauni mai muni ga kasar.

Darasin tabbatar da dimokaradiyya

Shugaban Najeriya na yanzu Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya na yanzu Muhammadu Buhari

To sai dai a tunanin Janaral Mansur Dan Ali Mai ritaya da ke zaman tsohon soja kuma ministan tsaron kasar a halin yanzu, babban darasi ya zuwa yanzu na zaman tabbatar da fifiko na demokaradiya bisa mulkin soja shekaru 50 bayan shigar da tsarin sojan cikin kasar. A nan Arewacin Tarrayar Najeriya inda ke bikin cika shekarun 50 dai, babbar matsalar na zaman maye makwafin Sardaunan da ma ragowar shugabannin da rayuwa da mulkinsu ke kama da mafarki. Hujjar kuma da a tunanin Adamu Chiroma ba ta rasa nasaba da irin salon mulkinsu.

Daga dukkan alamu dai al'ummar ta Arewa da ma kila daukacin kasar na shirin share 50 na gaba suna neman shugabancin da ba ruwansa da romo kan hanyar samun saukin lamura da kila sake dora kasar bisa hanyar dai-dai.

Sauti da bidiyo akan labarin