Shekaru 40 na juyin-juya halin Islama a Iran | Labarai | DW | 11.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekaru 40 na juyin-juya halin Islama a Iran

Kafin dai wannan rana shugaban na addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi zafafan kalamai ga Amirka sai dai ya sake jadadada cewa kalaman nasa raddi ne ga shugabanni.

Miliyoyin al'umma ne ake sa rai za su fita gangami a wannan rana ta Litinin a kasar Iran a yayin bikin tunawa da shekaru 40 na juyin-juya halin Islama da ya yi awon gaba da gwamnatin Shah Mohammed Reza Pahlavi da girka jagoranci na Shugaban addini Ayatollah Khomeini a shekarar 1979.

An dai tsaurara matakan tsaro a dukkanin fadin kasar gabanin gangamin bikin na Litinin. A shekara bara dai aka kai wani hari a lokacin da sojoji ke gudanar da wani maci. Harin da ya yi sanadi na rayukan mautane da dama.

Kafin dai wannan rana shugaban na addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi zafafan kalamai ga Amirka sai dai ya sake jadadada cewa kalaman nasa raddi ne ga shugabanni a Amirka ba al'ummar kasar ta Amirka ba.