Shekaru 40 da mutuwar Janar Murtala | Labarai | DW | 13.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekaru 40 da mutuwar Janar Murtala

A wannan Asabarce ake bikin cikar shekaru 40 da kisan gillar da aka yi wa Janar Murtala Ramat Muhammad, tsohon shugaban mulkin soji a Tarayyar Najeriya.

Murtala Muhammed

Murtala Muhammed

A ranar Asabar din nan ce aka gudanar da wata laccar tunawa da tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Janar Murtala Ramata Muhammad wanda aka yi wa kisan gillar a ranar 13 ga watan Febrerun shekarata 1976.

Daga cikin wadanda suka halarci taron laccar da aka gudanar a katafaren hotel din Hilton da ke a Abuja fadar gwamnatin Najeriya, sun hada da shugaban kasa Muhammadu Buhari gami da manyan wasu 'yan kasar.

A yayin juyayin tunawa da Murtalan masu gabatar da jawabai sun hada da Janar Julian Richard tsohon babban hafsan tsaron Britaniya da sakataren kungiyar ECOWAS.

Buhari ya ce, Najeriya ta yi babban rashi sakamakon kisan gillar da aka yi wa Janar Murtala. Ya ce Najeriya ta yi kuka sabili da marigayin ya yi duk abinda ya dace wajen dora kasar bisa ga turbar adalci da bin doka da oda.

'Yan Najeriya dai na kallon Janar Murtala Ramat Muhammad a matsayin zakaran gwajin dafi a jerin shugabanin da kasar tayi tun farkon tarihinta.