Shekaru 30 da faduwar katangar Berlin | Labarai | DW | 09.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekaru 30 da faduwar katangar Berlin

A yau ake shagulgulan zagayowar cika shekaru 30 da faduwar katangar Berlin, wacce ta kawo karshen cece-kuce da zaman rashin tabbas tsakanin al'ummomin Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma.

Daga cikin shugabannin kasashen da suka halarci bikin akwai Sulobakiya Poland Jamhuriyar Chek da Hungary na daga cikin manyan baki da suka kasance tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin a yayin bukin.

Baya ga wasu kasaitattun bukukuwan a yau din nan shi ma shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier ya gabatar da wani jawabi a gaban dandazon jama'a a kofar Brandebourg, a yayin da ita kuwa shugabar gwamnati Angela Merkel ta gabatar da  jawabinta a Bernauerstrasse, wurin da ke zaman matsirin soma ginin katangar ta Berlin da ta raba bangarorin biyu a ranar 13 ga watan Agustan 1961.

Sai dai masu sharhi na ganin wasu shugabannin manyan kasashen duniya abukan dasawar Jamus basa cikin wadanda suka halarci bukukuwan na wannan rana, a yayin da aka bayyana shugaban Faransa Emmanuel Macron da cewar zai halarci wata ganawa ne kawai a ranar Lahadi domin cin abincin dare da hukumomin na kasar Jamus, inda a share daya tuni sakataren harkokin wajen Amirka ya kammala ziyarar sa a yammacin jiya.

Sauti da bidiyo akan labarin