1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 20 da hadin kan kasa a Nijar

April 24, 2014

Hayaniyar siyasa ta dabaibaye bukukuwan hadin kan kasa a Nijar, shekaru 20 da rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta baiwa 'yan kasa fatan cewa lamura za su daidaita

https://p.dw.com/p/1Bo5v
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: Seyllou/AFP/Getty Images

A Jamhuriyar Nijar, ranar Alhamis ce ake bukukuwan tunawa da ranar da aka kebe ta hadin kan 'yan kasa, to sai dai sabgar na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar hayaniyar siyasa.

Kusan shekaru 18 kenan, da hukumomin kasar suka kebe wannan ranar da aka kebe domin hadin kan 'yan kasa a lokacinda aka kawo karshen tawayen Abzinawan arewacin kasar.

To saidai a 'yan shekarun baya bayan nan, kasar na fuskantar barazanar tashe tashen hankulla wadanda kuma kda nasaba da siyasa. Yanzu haka ma 'yan siyasar kasar sun sa karfe wuta ya kuma yi ja jawur tun lokacinda shugaba Issoufou Mahamadou ya bukaci kafa gwamnatin hadakar da zata kunshi ilahirin jam'iyoyin siyasar kasar, matakin da wasu ke ganin shi ne ya haddasa hayaniyar inji Mano dan Daraja daga jam'iyar MNSD Nasara.

Da dama ne dai daga cikin 'yan siyasar ke ganin matakin hada kan 'yan kasar na a matsayin wata wasar kwaikwayo kamar yadda alhaji Dangi na mai Fula daga jam'iyar Lumana ke cewa.

Tuareg-Truppen Mali
Gwamnatin Nijar ta kulla yarjejeniyar ne da AbzinawaHoto: picture alliance/Ferhat Bouda

Rashin gamsuwa da yanayin da ake ciki na hadin kan kasa

Daga na shi bangaren, Hamisu Dan Malam, daga jami'yyar PNDS Tarayya mai mulki, ya dora alhakin rikice-rikicen ne dake tasowa ga bangaren 'yan adawa yana mai cewa

To amman, ita Hajiya Oumma Ali, daga wata kungiyar mata, na mai kira ne ga 'yan siyasar da su maida banbance-banbancen na su a share daya su dubi fuskar kasar da ake dangatawa da kutal daga gare ki sai kura.

A can farko dai kasashen duniya na daukar kasar ta Nijar a matsayin wani dakin gwaje-gwaje a fannin demokradiya wanda idan ba a kiyaye ba sannu a hankali zai rugujewa.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Pinado Abdu Waba