Shekaru 20 da fara aikewa da sakonnin SMS | Zamantakewa | DW | 05.12.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shekaru 20 da fara aikewa da sakonnin SMS

Masana na bayyana alfanun da ke tattare da tsarin SMS wajen isar da sakonni cikin sauki da kuma irin ci gaban da tsarin ke samu a baya bayannan.

Tsarin gajeren sakon SMS da aka kirkiro da shi a shekarun 1980 dai, an kai ga kaddamar da shi ne a shekara ta 1992, inda masu tu'ammuli da wayar tafi da gidanka ke aikewa da sakonnin su cikin haruffan da basu zarta 160 ba ga kowane sako guda daya, wanda kuma wadanda suka bullo da tsarin ke ganin ya wadatar wajen isar da sakon da ake bukata.

Anan Jamus dai alkaluma na nunar da cewar sau dai-dai har miliyan dubu 46 ne masu tu'ammuli da wayoyin sadarwar tafi da gidanka suka aike da sakonni a shekarar da ta gabata, abinda ke tabbatar da cewar aikewa da sakonnin SMS din ya zama wani bangare ne na rayuwar jama'a ta yau da kullum. Idan aka kiyasta hakan, za'a ga cewar a kowace rana kowane Bajamushe guda na rubuta sakonnin SMS biyu ne domin isar da wani sako: Ko dai zai makara wajen dawowa daga wurin aiki, ko neman lokacin ganawa ko kuma aikewa da jerin abubuwan da za'a sayo daga shaguna. Sai dai kuma ba'a yi hangen cewar gajeren sakonnin zai sami irin wannan nasarar ba a lokacin kirkiro da tsarin.

A dai ranar ukku ga watan Disambar shekara ta 1992 ne aka aike da sakon farko ta hanyar SMS a duniya, wato shekaru 20 kenan yanzu haka. Sai dai kuma ko da shike wayar salular da ake anfani da ita a wancan lokacin kusan farashinta yakai na kudi Euro dubu daya da 500, amma ba ta iya tura sakon, saboda haka ta hanyar na'urar Computer ne aka aike da sakon farko wanda ke taya murna game da bukin Kirsimeti. A wancan lokacin, Injiniyoyin kanfanin wayar sadarwar Vodafon ne aka baiwa damar yin gwajin, wanda a cewar Rafaela Moeh na kanfanin dake samarwa jama'a hanyoyin Internet ya daga martabar kanfanin:

" Wannan shine abinda ya taso a tsarin sadarwa. Sai kuma aka bullo da sabuwar dabarar da za'a gabatarwa masu anfani da wayoyi a matsayin wata hidima a garesu. Saboda hakane ma a wasu wurare ake bayar da hidimar kyauta."

Sai dai kuma hakan ya sauya cikin dan karamin lokaci, domin kuwa a yanzu masu tu'ammuli da wayoyin sadarwa na biyan kudin aikewa da sakonnin SMS, wanda kuma ke samar da dimbin kudaden shiga ga 'yan kasuwa da kanfanonin sadarwa. Sai dai tambayar anan itace har zuwa wani lokaci ne za su ci wannan gajiyar, bisa la'akari da yaduwar sabbin hanyoyin aikewa da sakonni ta wayar salula irin ta zamani wadda aka fi sani da suna Smartphones? Urs Mannsmann, Editan mujallar da ake bugawa ta yanar gizo mai suna C-t, ya ce tuni kanfanonin sadarwar suka fara ganin tasirin hakan:

" A halin da ake ciki kanfanonin sadarwa na baiwa masu anfani dasu kayyadadden farashi na aikewa da sakonnin SMS, shine yasa yawan SMS da ake aikewa a yanzu bai raguwa kuma bai karuwa kuma cinikin masu bayar da layuka na bunkasa."

Sabbin hanyoyin aikewa da sakonni irinsu WhatsApp da wanda masu harka da iPhones ke yin anfani dasu dai na basu damar aikewa hatta da hotuna da kuma bidiyo, baya ga rashin kayyade musu tsawon sakonnin da za su aike sabanin yanda lamarin yake a da ga wadanda ke yin anfani da wyoyin da ba su da wannan fasahar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal

 • Kwanan wata 05.12.2012
 • Muhimman kalmomi SMS
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16w7h
 • Kwanan wata 05.12.2012
 • Muhimman kalmomi SMS
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16w7h