1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 17 da kai harin ta'addanci a Amirka

Gazali Abdou Tasawa
September 11, 2018

A kasar Amirka an cika shekaru 17 da kasar ta fuskanci hare-haren ta'addanci na kungiyar Al Ka'ida na ranar 11 ga watan Satumban 2001 da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin dubu uku.

https://p.dw.com/p/34eUr
USA New York Anschlag auf das World Trade Center
Hoto: picture-alliance/AP Photo/C. Soi Cheong

Albarkacin wannan rana Shugaba Donald Trump zai kai ziyara a birnin Shanksville na jihar Pennsilvaniya inda daya daga cikin jiragen saman da kungiyar Al-Ka'idan ta yi amfani da su wajen kai harin ya fado a cikin wata gona ta bakin birnin, bayan da fasinjojin da ke cikin jirgin suka yi kokarin kwace shi daga hannun 'yan ta'addan domin hana masu kai harin kan ginin majalissar dokokin kasar na Capitole.  

Shugaba Trump zai kai ziyarar ce a birnin domin karrama kushewar mutanen da suka rasu a cikin hare-haren na ranar 11 ga watan Satumban 2001, da kuma musamman ta fasinjojin jirgin mai lamabar tafiya ta 93, wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen hana wa 'yan kungiyar ta Al-Ka'ida kai harin a ginin majalisar dokokin ta Amirka, bayan da ta waya suka samu labarin cewa an kai wasu hare-haren da jiragen sama a gine-ginen babbar cibiyar cinikayya ta duniya ta Word Trade Center da ke a birnin New York.