Shekaru 15 bayan harin 9/11 | Labarai | DW | 11.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekaru 15 bayan harin 9/11

A yau ne a a Amirka ake bukukuwan tunawa da hare-haren ta'addancin na 11 ga watan Satumban shekarar 2001 inda mutane sama da dubu uku suka rasu.

Harin dai ya afku ne a gine-ginen cibiyar kasuwancin nan ta World Trade Center da kuma hukuar tsaron Amirka din ta Pentagon. Shugaba Barack Obama na Amirka ya ce abubuwa da dama sun sauya a shekaru 15 da suka gabata. Amirka karya kashin bayan 'yan al-Qaeda da suka kai harinsannan an tsaurara matakan tsaro a cikin gida wanda hakan ya sanya muka magance kai hare-hare don kiyaye rayukan al'umma.

Za dai a gudanar da addu'o'i a majami'u da wasu wurare na musamman da aka kebe don tunawa da wanda suka rasu a harin na 11 ga watan Satumba wadda aka bude a shekarar 2011 muma daga wannan lokaci zuwa yanzu kimanin mutane miliyan 23 ne suka ziyarci wannan waje.