1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 10 da fara rikicin Boko Haram a Najeriya

Mohammad Nasiru Awal SB
August 1, 2019

Rikicin Boko Haram ya haifar da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a ciki da wajen Najeriya, tare da yada akidar kungiyar a wasu kasashe makwaftan kasar.

https://p.dw.com/p/3N92M
Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Hoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Yayin da aka ciki shekaru 10 da fara rikicin Boko Haram bayan kashe shugabanta na farko Muhammad Yusuf da jami'an tsaro suka yi lokacin yana hannunsu, har yanzu an kasa kawo karshen rikicin. Ana iya cewa kashe jagoranta ya haifar da rikicin na Boko Haram da aka kwashe shekaru 10 ana fama da shi wanda ya bazu zuwa wasu jihohin Najeriya da ma kasashen makwabta kamar Chadi da Kamaru gami da Jamhuriyar Nijar.