1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 10 da bala'in Tsunami

December 26, 2014

Al'ummomin kasashen da bala'in Tsunami ya afaka musu shekaru 10 da suka gabata na gudanar da addu'oin tunawa da 'yan uwa da abokan arzikin da suka rasa rayukansu.

https://p.dw.com/p/1EAMk
Hoto: Reuters/Beawiharta

Bala'in na Tsunami dai an bayyana shi a matsayin mafi muni da ya taba afkuwa a duniya baki daya. Mutane dubu 220 ne dai suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da tekun Indiya ya yi hade da mummunar girgizar kasa a ranar 26 ga watan Disamba na shekara ta 2004. Kasashe 14 ne wannan bala'i ya shafa da suka hadar da Indonesiya da Thailand da Sri Lanka. An dai gudanar da addu'oi a Masallatai a yankin Tsibirin Aceh da ke yankin Sumatra na kasar Indonesiya, yayin da mutane ke kai ziyara kabarurrukan wadanda suka rasa rayukansu a yayin bala'in na Tsunami, cikin yanayi na alhini da kuma zubar da hawaye.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar