Shekaru 10 da aukuwar bala′in Tsunami | Siyasa | DW | 26.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 10 da aukuwar bala'in Tsunami

Gabanin bala'in na Tsunami a shekarar 2004, lardin Aceh na kasar Indonesiya ya kasance wani yanki na yakin basasa. Amma yanzu zaman lafiya ya wanzu.

Banda Aceh Moschee Flut Indonesien Tsunami Archiv

Masallacin Banda Aceh lokacin Tsunami a 2004

Shekaru 10 da suka gabata da safiyar ranar 26 ga watan Disamban shekara ta 2004 aka samu girgizar kasa a karkashin teku da ta haddasa bala'in Tsunami, da dubban mutane suka hallaka a wasu kasashen Asiya.

Girgizar kasar mai karfin maki 9.1 ta ratsa gaban ruwan yankin Aceh na kasar Indonesiya, inda a gaba daya fiye da mutane 220,000 suka hallaka a kasashe 14. Lamarin ya kai har zuwa kasashen Sri Lanka da Indiya, da kuma Somaliya a Afirka. Kasar Indonesiya ke kan gaba inda bali'in ya ritsa da rayukan mutane kimanin 170,000.

A Lardin Aceh na kasar ta Indonesiya kusan mutane 130,000 suka hallaka sakamakon bali'in na Tsunami a 2004, abin da ke zama mafi girma a wuraren da bali'in ya shafa.

Sake gina yankunan da Tsunami ta latata

Bildergalerie 10 Jahre Tsunami Indonesien

Banda Aceh shekaru 10 bayan Tsunami

Lardin na Aceh yana yankin arewacin Sumatra, kuma lokacin da lamarin ya faru igiyar ruwa da ta tashi ta kai tsawon mita 35, abin da ya haddasa mutuwar mutane. Sai dai yanzu bayan kashe makudan kudade, an sake gina wuraren da bali'in Tsumani ya lalata.

Felix Heiduk masani kan harkokin da suka shafi Indonesiya a gidauniyar kasuwanci da siyasa ta birnin Berlin, ya ce taimakon da aka bayar ya taimaka.

"An sake gina gidaje, cikin hanzari komai ya ingata kamar yadda suka yi ta gani. Wanda ya ziyarci Aceh yanzu idan ya kwatanta da kafin Tsunami, lallai zai ga yadda aka mayar da komai na zamani."

Ingantuwar rayuwa a Aceh

Zehn Jahre nach Tsunami in Banda Aceh Indonesien

Addu'ar tunawa da wadanda bala'in ya rutsa da su

Gwamnatin kasar Indonesiya da kasashen duniya masu ba da taimako sun kashe fiye da dala biliyan bakwai wajen sake gina yankunan da aka samu bala'in na Tsunami. A yankin Aceh an yi amfani da kudaden wajen mayar da yankin ya dace da gine-gine da rayuwa na zamani, abin da za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu.

Kamar yadda Alex Flor na kungiyar kare hakkin dan Adam da ke saka ido kan Indonesiya yake cewa:

"A shekaru goma da suka gabata harkokin rayuwa a Aceh komai ya inganta."

Kusan daukacin kasashen Asiya da suka fuskanci bala'in Tsunami sun yi kokari kan inganta rayuwa, sannan an saka na'urar ba da gargadi kan yiwuwar samun Tsunami, saboda kare sake samun mutuwar mutane irin na shekara ta 2004. Har yanzu mutanen da abun ya shafa suna tunawa da irin mawuyacin halin da suka shiga da mutuwar 'yan uwa da abokan arziki.

Sauti da bidiyo akan labarin