1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shekaru 10 da kungiyar NATO ta shiga rikicin Libiya

Mohammad Nasiru Awal SB
March 19, 2021

A shekarar 2011, shekara 10 ke nan da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta tallafawa kungiyoyin tawayen kasar Libiya, wadanda suka tayarwa tsohon shugaban kasa Muammar Gaddafi kayar baya.

https://p.dw.com/p/3qs8J
Deutschland Berlin | Demonstranten | Libyen Konferenz
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Zinken

A shekarar 2011, shekara 10 ke nan da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta tallafawa kungiyoyin tawayen kasar Libiya, wadanda suka tayarwa tsohon shugaban kasa Muammar Gaddafi kayar baya. Ko da yake kutsen ta NATO ta yi ya kai ga kifar da gwamnatin Gaddafi da ma kashe shi, amma fatan da aka danganta shi da katsalanda bai cika ba.

Konflikt in Libyen
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Salahuddien

An yi fata tawayen da aka yi shekaru 10 da suka wuce ya kawo sauyi. A cikin watan Fabrarirun 2011 'yan kasar Libiya sun bi takwarorinsu na wasu kasashen Larabawa, sun fantsama kan tituna don nuna adawa da gwamnatin Shugaba Muammar Gaddafi, wanda ya yi mulkin kama karya tsawon shekaru 40. Boren ya rikide zuwa rikici soji, inda wani sashe na rundunar kasar ya koma bangaren masu zanga-zanga, dayan kuma ya ci gaba da yi wa Gaddafi biyayya.

Rikicin ya rincabe. A ranar 17 ga watan Maris na 2011 Majalisar Dinkin Duniya ta amince a dauki matakan soji a rikicin na Libiya don ba wa al'umar kasar kariya tare kuma da mara wa masu adawa da Gaddafi. Kwanaki biyu bayan haka, wato 19 ga watan Maris kasashen Amirka da Birtaniya da Faransa suka fara lugudan wuta ta sama kan dakarun Gaddafi, sannan a ranar 31 ga watan na Maris kungiyar tsaro ta NATO ta karbi ragamar farmakin har zuwa watan Oktoban shekarar ta 2011 lokacin da ta kwace birnin Sirte da ke zama mahaifar Gaddafi, sannan ranar 20 ga watan 'yan tawaye suka kama shi suka kuma halaka shi.

'Yan siyasar kasashen yamma sun dauki mutuwar Gaddafi a matsayin wata dama ta bude sabon babi ga kasar ta Libiya, kamar yadda a ministan harkokin wajen Jamus a lokacin, Marigayi Guido Westerwelle ya nunar da irin ta'asa da tsohuwar gwamnati ta aiwatar.

Konflikt in Libyen
Hoto: picture-alliance/XinHua/A. Salahuddien

Sai dai wannan fatan bai cika domin ba a kawo karshe tashe tashen hankulan a Libiya ba, rikicin ya koma yakin basasa na tawon shekaru. A dangane da haka ana iya cewa katsalandan na NATO bai cimma burinsa ba, inji Thomas Claes daraktan gidauniyar Friedrich-Ebert da ke kasar Tunisiya wanda yake ganin tabbas katsalandan NATO ya sa an kawo karshen cin zarafin dan Adam karkashin Shugaba Gaddafi da gwamnatinsa ko ma a ce an rage shi. Dole ne a san cewa babban laifin na a kan manufofi da aika-aikar da aka yi a zamanin mulkin Gaddafi, amma ba a kan katsalandan da NATO ta yi ba.

Libiya dai ta zama wani fagen yaki da wasu manyan kasashen duniya ke da hannu ciki. Amma a watanin baya bayan nan Majalisar Dinkin Duniya ta dukufa ta kuma shawo kan masu rikici su tsagaita bude wuta. A farkon watan Fabarairu an cimma matsaya a taron Majalisar Dinkin Duniya, inda wakilai suka amince da kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta shirya zaben majalisar dokoki a cikin watan Disamba, tare da samar wa kasar kundin tsarin mulki da sabuwar dokar zabe. Yanzu kasar ta samu sabon Firaminista, Abdel-Hamid Dbeibah wanda tuni ya kafa gwamnati mai ministoci guda 30 da suka fito daga dukkan bangarorin da ke rikici da juna a kasar ta Libiya.