Shekara guda na mulkin Boubacar Keita a Mali. | Siyasa | DW | 04.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekara guda na mulkin Boubacar Keita a Mali.

Bayan fama da matsalolin tawaye al'ummar kasar Mali na da kwarin gwiwa kan makomar kasar bayan da ta sake komawa tafarkin dimokradiya.

Karya lagon tsohon shugaban mulkin sojan kasar Amadu Sanogo da jefa shi gidan yari tun farkon hawansa mulki, tare da ayyana shekarar 2014, a matsayin shekarar yaki da cin hanci da karbar rashawa, abubuwa ne da suka kara wa shugaban farin jini, duk da an kama wasu mutane, rashin kama cikakkun barayin kasar ta Mali ya sa al'umma shakku kan cika alkawarin na shugaba Ibrahim Boubacar Keïta .

Wata matsalar da gwamatin Keïta ke famada ita ita ce ta rashin iya sadarwa don nuna wa 'yan kasar ta Mali kokarin da gwamnatin ke yi musamman idan aka lura da bukatu da dama da 'yan kasar ke fatan gwamnatin ta share musu hawaye cikin gaggawa, wanda lokacin yakin neman zabensa takensa shine: "Mali itace farko,kare 'yan Mali da jin dadinsu" abinda Amadu Koita wani jigo a jam'iyyar adawa ta PS yelen kura ya soki shugaban da cewa yanzu duk wasu kwangiloli sai danginsa dana kusa da shi, harakar mulkin ta koma ta gida, wanda ya koka da karin kudin wuta da ruwa da gwamnatin ta Keïta ta yi, ga kasa magance matsalar arewacin kasar musaman garin Kidal. Amina traore wata yar kungiyar farar hulla na mai ra'ayin cewa a shekara daya shugaban bai iya magance matsalolin kasar Mali:

"Ibrahim Bubakar Keita ya gaji kasar Mali ce cikin rikici mai sarkakiya da kuma tsanani,bai yiwuwa a watanni sha biyu kadai a magance matsalar 'yan tawaye da masu kishin Islama, yanayin kasar Mali fa bai da banbanci da matsalolin da sauran kasashen Afirka da suke fuskanta"

Al'ummar arewacin kasar sun ce gwamnatin IBK ta musu faduwar toto ruwa, ganin yanzu haka a garuruwan Kidal, Gao da Tombouctou fita wajen gari nada hadari sosai, babu tsaro duk da kasancewar dakarun tabbatar da tsaro na Munisma da Barkhane, amma 'yan bindiga dadi ke cin karensu babu babbaka.

A cewar Mumuni Sumanu malamin makaranta a jami'ar Bamako sojojin Mali na da matsaloli da dama:

"Akwai dakarun Mali da dama dake daukar horo yanzu haka tare da taimakon kasar Faransa da tarayyar turai, amma ko shakka babu sojojin Mali na fuskantar matsaloli masu tarin yawa, babu kayan aiki isassu kuma na zamani, sannan siyasa na taka rawa wajan nada shugabannin sojan da ba su da kwarewa, dubi abin kunya da wulakanci tare da kisan gillar da 'yan tawaye a Kidal su kai wa dakarun gwamnati"

Rashin kai ziyarar shugaba Ibrahim Bubakar Keita tun hawansa a garuruwan Kidal, Gao da Tombouctou mazauna yankin na ganin shugaban babu ruwansa da su, abinda yawancinsu ke ganin makomar yankunansu ta dogara ne da tattaunawar da ake yanzu haka a birnin Algiers ba daga Bamako ba.

Mawallafi:Salissou Issa
Edita: Yusuf Bala

Sauti da bidiyo akan labarin