Shekara guda da sace ′yan matan Chibok | Labarai | DW | 14.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekara guda da sace 'yan matan Chibok

'Yan matan makarantar garin Chibok dake a arewacin Najeriya sun cika shakara guda da shiga hannun kungiyar Boko Haram.

Yau Talatar nan ce 'yan matan makarantar Chibok ta arewa maso gabashin Najeriya ke cika shakara guda da shiga hannun kungiyar 'yan bindigan nan ta Boko Haram.

Sakamakon hakan ne kuwa kungiyoyin sassan duniya da ke fafutukar kwato su, suka tsara gangami daba-daban na tunawa dama matsawa hukumomin Najeriya don kwato wadannan 'yan makaranta.

Yanayin da ake ciki dangane da 'yan matan na Chibok kimanin 220 da Boko Haramun din ta yi garkuwa da su dai, na zuwa ne yayin da kungiyar hare hakkin nan ta kasashen duniya, Amnesty Int'l, ke cewa kawo i yanzu, mayakan na Boko Haram sun sace akalla manyan mata da 'yan mata 2000, tun farkon wannan shekara zuwa wannan lokaci.

A birnin New York na Amirka ma dai akwai wani reshen kungiyar fafutukar matsin lambar kwato su ta #BringBackOurGirls, saboda tunawa da 'yan matan, ya zage da kiraye-kiraye a dai dai wannan lokaci a gangamin musamman zai gudanar a Amirkar.