Shekara guda bayan kare yakin Gaza | Siyasa | DW | 29.12.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekara guda bayan kare yakin Gaza

Yan Israila sun juya hankalin su kan kasar Iran, shekara guda bayan da aka kare yaki a Gaza

Shugaban Palesdinawa, Mahmud Abbas

Shugaban Palesdinawa, Mahmud Abbas

A yayin da mafi yawan mazauna yankin Gaza har yanzu suke fama da matsananciyar wahala sakamakon mamayewa da toshe yankin su da Israila tayi, amma ga mazauna Israila din yakin Gaza abu ne da ya zama tarihi

Schlomi Eldar ya kasa mantawa da yakin da ya gudana a yankin Gaza, saboda haka ma ya shirya wani film da zai nunar da yadda dangantaka take, tsakanin yan Israila da Palesdinawa. Dan jaridar yana fatan nuna wannan film cikin watan Fabrairu a lokacvin bikin nunin fina-finai na Berlin da ake kira Berlinale.

Tsawon shekaru ashirin Schlomo Eldar yana gabatar da rahotanni daga yankin Gaza, tareda bankado al'amura fiye da ko wane dan jarida na Israila. Duk da haka yace wnnan yaki na Gaza abu ne da ya dace, saboda haka ma sukan da yayi wa matakan Israila a yankin na Gaza lokacin yakin bai zama mai tsanani ba.

Yace ina ganin cewar wani bangare na yan Israila suna da ra'ayin cewar wataklila Israila ta gwada karfin da ya wuce gona da iri a lokacin yakin a Gaza, saboda yawan wadanda suka mutu a yakin na Gaza sun kai 1400. Ina ganin duk da burin Israila na kawo karshen hare-haren rokoki daga yankin na Gaza, amma mun wuce gona da iri.

Daga hbangaren Israila kuwa, ana ganin yakin ya sami matukar nasara. Tun bayan kawo karshen sa hare-haren rokokin daga Gaza zuwa Israila sun ragu da misalin kashi casa'in cikin dari. To sai dai duk da haka, ana ci gaba da samun hare-hare na rokoki samfurori dabam dabam a kullum daga yankin. Tun bayan yakin Palesdinawa sun harba rokoki har sau dari biyu da arba'in da biyu zuwa Israila. Yan kalila ne daga cikin su suka sauka a wuraren da mutane suke zaune, babu kuma mutum ko daya da ya rasa ransa. A daya hannun, sojojin Israila sun kai hare-hare 143 zuwa Gaza, musamman a wurare malakar Hamas da hanyoyi na karkashin kasa da akan yi amfani dasu domin sumogar makamai da kan su kansu yan sari ka noke na Palesdinawa. Hukumar kididdiga ta rundunar sojan Israila taki baiyana yawan Palesdinawan da suka mutu sakamakon wadannan hare-hare.

Saboda haka ana iya cewar yaki tsakanin Palesdinawa da Israila dai bai kare ba, duk da haka mazauna yankunan na Palesdinawa da na Israila suna ganin al'amura yanzu dai sun dan sassauta.

Tashin hankali yana iya sake tabarbarewa a ko wane lokaci a yankin na Gaza. Rundunar sojan Israila ma tace tana shiryawa yiwuwar sake tashin yaki karo na biyu a yankin tsakanin ta da Hamas. A nasu bangaren yan kungiyar ta Hamas sun yi amfani da shekara guda tun bayan kawo karshen yakin domin kara daurawa kansu damarar makamai, inmda ma suke gwada wasu rokoki dake iya kaiwa nisan kilomita 60 daga inda aka harba su. Wato a takaice nan gaba suna iya sauka Tel Aviv ko a tashar jiragen saman Ben Gurion.

Yan Israila kusan a ce sun manta da yakin Gaza, inda a garesu, wannan al'amari ne da ya faru kuma ya wuce. Abin da suke gani shine: yakin dai ya zama wajibi kuma an yi shi, an kuma sami nasarar sa. Babban abin dake damun su a zuciya shine, yiwuwar harin makaman nuclear Iran zuwa kasar ta Israila. Jael misali, mai wnai dan karamin kantin sayar dfa taba a Tel Aviv dake cewa:

Babu shakka ina zaune ne cikin tsoro. Ina cikin tsoro matuka, kuma ina fata ba za'a kai matsayin da har za'a kawo mana irin wnanan hari ba. Ina fatan za'a dauki lokaci mai tsawo ba'a kai ga haka ba.

A daya hannun, mai sharhi cikin jaridar Haaretz Aluf Benn yace wajibi ne duka yan Israila su yarda da cewar zasu ci gaba da fuskantar barazanar nuclear daga Iran saboda babu mai iya sanin irin barnar da zata biyo bayan duk wani hari da Israila zata kai kan tashoshin nulea da kasar Iran din take mallaka.

Maawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Halimatu Abbas