Shekara daya da rasuwar Mandela | Siyasa | DW | 05.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekara daya da rasuwar Mandela

Afrika ta Kudu ta gudanar da bikin tuna marigayi Nelson Mandela. Tsofaffin 'yan gwagwarmayar yaki da mulkin danniya sun halarci bukin da aka yi a birnin Pretoria.

Tare da busa algaitar vuvuzela tsawon mintuna uku da dakika bakwai kafin a yi shiru na mintuna uku aka yi jimamin mutuwar Nelson Mandela, wanda ya rasu a ranar biyar ga watan Disamban shekarar 2013. Mintuna shida da dakika bakwai din na matsayin shekaru 67 da Mandela ya bauta wa Afirka ta Kudu a matsayin dan gwagwarmaya, firsina da kuma dan siyasa. Daukacin al'ummar Afirkan ta Kudu na daukar bikin na wannan Jumma'a a matsayin jan hankalinsu. Domin shekaru 20 bayan zaben gama gari na farko, kasar na cikin wani wadi na tsaka mai wuya.

Yanayin siyasar Afirka ta Kudu bayan Mandela

Ba a kai wata guda da aukuwar hayaniya a zauren majalisar dokokin kasar ba, lokacin da 'yan adawa na jam'iyyar Economic Freedom Fighters suka

kira shugaban ANC barawo mai aikata laifi. Bayan an kasa shawo kan lamarin, 'yan sanda a cikin damarar yaki sun yi wa zauren dirar mikiya, inda aka ba wa hamata iska. Wani mai fafatukar kare hakkin jama'a Lawson Naidoo ya ce irin wananan badakala ba za ta taba faruwa lokacin Mandela ba.

"Ba mu taba tunanin ganin irin wadannan hotuna cikin wata al'umma mai bin tsarin demokradiyya ba. Mun cikin wani hali na tsaka mai wuya, domin majalisar dokoki da sauran hukumomin demokradiyya da na jama'a suna cikin mawuyacin hali."

Rashin gamsuwa da yanayin mulki a Afirka ta Kudu

Naidoo dai shi ne daraktan majalisar ci-gaban tsarin mulkin Afirka ta Kudu wato CASAC da ke zama matattarar masu nunan rashin gamsuwa da halin da kasar ke ciki. Cikin 'ya'yan wannan majalisa akwai 'yan jam'iyyar ANC. Hatta a cikin jam'iyyar an kasa dawo da shugaban kasa Jacob Zuma kan turba. Ga misali da kudin kasa aka

sabunta gidan shugaban da ke kauyensu. Kuma bayan binciken da aka yi na wannann badakala, umartarsa aka yi da mayar da wani kaso na kudin. Ga 'yan adawa wannan hukuncin na zaman cin fuska. Afirka ta Kudu dai na rashin kyakkyawan shugabanci, inji lauya kuma mai fafatukar kare hakkin jama'a Lawson Naidoo.

Afirka ta Kudu ta yi rashi

"Afirka ta Kudu na bukatar kyakkyawan shugabanci ba fadar shugaban kasa kadai ba. Muna bukatar shugabannin kwarai a dukkan fannoni, wadanda za su yi wa al'umma jagoranci na gari bisa tsarin mulkin kasa, da bin tafarkin demokradiyya tsantsa, amma ba wata gwamnati da abin da ta sa gaba shi ne kare muradun jam'iyya da 'ya'yan jam'iyya daga fuskantar hukuncin da doka ta tanadar ba."

Bikin cika shekara daya da mutuwar Nelson Mandela zai ba wa 'yan Afirka ta Kudu damar yin waiwaye ga tafiyar hawainiya da ake samu wajen aiwatar da canje-canje tun shekarar 1994. Kashi daya bisa hudu na majiya karfi a kasar suna zaman kashe wando yayin da kashi 60 cikin 100 na matasa a kasar ba su da aikin yi, gibi tsakani talaka da mai kudi na karuwa, abin da ke janyo yawaita aikata laifi da tashe-tashen hankula.

Sauti da bidiyo akan labarin