Shekara daya da aukuwar ambaliyar igiyar ruwan Tsunami | Labarai | DW | 25.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekara daya da aukuwar ambaliyar igiyar ruwan Tsunami

An fara gudanar da bukukuwan zagayowar shekara guda da aukuwar mummunar ambaliyar igiyar ruwan ta Tsunami a Thailand da kuma wasu kasashen yankin Asiya. A jiya asabar wadanda suka tsira daga wannan bala´i da kuma ´yan´uwan wadanda suka rasu sun ajiye furanni tare da yin addu´o´i a tsibirin Phuket dake kasar Thailand. Kimanin mutane dubu 230 aka kiyasce sun rasu sakamakon bala´in na ambaliyar igiyar ruwan da ta auku kasashen dake gabar tekun Indiya a ranar 26 ga watan desamban shekara ta 2004.