1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar waɗanda ake zargi da yunƙurin kifar da gwamnatin Turkiyya

August 5, 2013

A duk cikin hukunce-hukuncen da aka yanke, hukuncin ɗaurin rai da ran da aka yankewa fitaccen tsohon hafsan sojin ƙasar Ilker Basbug ya fi sosawa 'yan ƙasa rai

https://p.dw.com/p/19K2V
Lawyers and media members wait to enter a courthouse in Silivri, where a hearing on people charged with attempting to overthrow Prime Minister Tayyip Erdogan's Islamist-rooted government is due to take place, August 5, 2013. A Turkish court on Monday began sentencing nearly 300 defendants accused of plotting to overthrow the government, handing prison sentences of up to 20 years to some and acquitting 21 others. The court was announcing the verdicts individually. Verdicts on high-profile defendants including former armed forces commander Ilker Basbug were yet to be announced. REUTERS/Murad Sezer (TURKEY - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Masu zanga- zanga a gaban kotuHoto: Reuters

Wata Kotu a Turkiyya ta fara yanke hukunci a shari'ar nan mai sarƙaƙiya ta mutane 275 waɗanda ake zargi da yunƙurin kifar da gwamnatin ƙasar.

A na ma wannan shari'ar kallon wata zakarar gwajin dafin ƙwarin dangantakar Firaminista Recep tayip Erdogan da masu rajin kafa gwamnatin da ba ruwanta da addini da dakarun sojin da ke adawa da shi.

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun ce an wanke 21 daga cikin waɗanda ake zargin, an kuma yankewa ɗaya daga cikin manyan tsoffin hafsoshin sojin ƙasar mai suna Ilker Basbug hukuncin ɗaurin rai dai rai a gidan kaso, da ma wani hukuncin ɗaurin shekaru 35 wa wasu 'yan majalisa 'yan adawa su 12.

Jama'a dai sun harzuƙa a wajen kotun da shari'ar ke gudana cikin matakan tsaro masu tsauri a garin Silivri da ke kusa da Santanbul, kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa 'yan sanda sun yi amfani da hayaƙi mai sanya hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zanga, waɗanda suka kawar da shingen da jami'an tsaro suka killace kotun da shi, da nufin faɗawa Kotun ko ta halin ƙaƙa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal