Shari′ar matar tsohon shugaban Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 29.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shari'ar matar tsohon shugaban Cote d'Ivoire

Kotun kasar Cote d'Ivoire ta yi watsi da batun cewa tsohon Shugaba Laurent Gbagbo da ke kotun duniya na cikin 'yan takara

Mahukuntan kasar Cote d'Ivoire na shirin gabatar da Simone Gbagbo matar tsohon Shugaba Laurent Gbagbo a gaban kotu tare da jiga-jigan tsahuwar jam'iyya mai mulki ta FPI guda 82, wadanda ake zargi da laifukan cin amanar kasa. Tuni kotun kasar ta yi watsi da gabatar da Laurent Gbagbo wanda yake fuskantar tuhuma a kotun duniya, a matsayin dan takara a zaben da ke tafe.

Tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2010 ya kai ga mutuwar mutane kimanin 3000.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar