Shari′ar Dasuki tare da boye shedu ta dauki hankali a Najeriya | Siyasa | DW | 26.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shari'ar Dasuki tare da boye shedu ta dauki hankali a Najeriya

A yanayin da ke nuna daukan sabon salo da shari’ar ake yi wa tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara a harkar tsaro lauyoyin gwamnati sun gabatar da sabbin tuhume-tuhume da suka hada da na safarar kudade.

Nigeria Sicherheitsberater Sambo Dasuki

Sambo Dasuki tsohon mai bada shawara ga tsohon shugaba Jonathan a Najeriya

To sabbin tuhumar da ake yiwa Kanal Sambo Dasuki da aka karanta masa a gaban mai shari'a Adeniyo Ademola na babbar kotun da ke Abuja dai sun hada da zargin sa da mallakar dala dubu 40 da kuma Naira milyan biyar a gidansa da ke Abuja, da kuma wasu kudaden Naira milyan 37.6 da ma dala dubu 150 a Sokoto, wanda ya nuna kari a kan zarge-zargen da ake masa wanda ya saba dokar safarar kudade da mallakarsu ta hanya da ba ta dace ba a Najeriya

Duka laifuffukan da ake zargin Kanal Dasuki da aikatawa da yanzu suka kai guda biyar dai ya musanta zargin a gaban kotun bayan da aka karanta masa su. Sauya yanayin tuhuma ya kasance abin da ya dauki hankali, musamman yadda a yanzu batun ya hada da batun almundahanar kudade. Yunus Abdulsalam na cikin layoyin da ke cikin tawagar ta Kanal Dasuki.

Nigeria Präsident Amtseinführung von Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya na kama rantsuwar aiki

" Bisa tsarin shari'a gabatar da bukatar sabunta tuhume-tuhume na zargin da ake yi abu ne da aka saba da shi a shari'a irin wannan. Domin dokar hukunci a kan manyan laifuffuka ta bada dama anan, don haka idan masu tuhuma sun ga suna da bukatar yin haka abu ne da doka ta amince da yin haka kamar yadda na ce''.

Wannan tuhuma dai na daya daga cikin shari'oin da gwamnatin Najeriyar ke yi da ke daukan hankalin jama'a musamman ma dai yakin da take yi da cin hanci da rashawa da ya shafi manyan mutanen da suka rike mukamman gwamnati, abinda ya sanya masharhanta bayyana bukatar jajircewa sosai wajen yaki da cin hanci da rashawa.

A yayinda lauyan gwamnati da ke tuhumar ya ki cewa uffan a kan wannan tuhuma, gabatar da bukatar boye mutanen da za su bada shaida a shari'ar ta Dasuki na zama abin da ke kara jefa tambaya dalilin wannan bukata, sanin cewa a shari'ar da ta shafi ta'adanci ne aka fara ganin hakan a Najeriya. Ko yaya lauyoyin suka dauki lamarin? Har ila yau ga Barrister Yunus Abdussalam.

" A gaskiya ba abu ne da aka saba gani ba a ce a shari'a irin wannan ta zargin mallakar makamai da almundahnar kudade a ce ana neman boye shaidu abu ne na mamaki. To sai dai tunda Magana na gaban kotu, to kotun ce ke da ikon yanke hukunci, mun yi imanin cewa kotu ce za ta yanke hukunci a kan wannan".

A yanzu za'a sa ido a ga inda za ta kaya a kan wadannan sabbin tuhuma da gwamnatin Najeriyar ta bullo da su a wannan shari'a, wacce alkali Adeniyi Ademola ya tsayar da ranar Laraba 28 ga watan nan domin ci gaba da shari'ar.

Sauti da bidiyo akan labarin