1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar cinikin jarirai a Nijar

November 25, 2014

A Jamhuriyar Nijar alkalin kotun daukaka kara a birnin Yamai ya bada belin wasu daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a cikin badakalar cinikin jarirai daga Najeriya.

https://p.dw.com/p/1Dtff
Hoto: DW/S. Boukari

An dai ba da belin mutanen ne bayan sun kwashe watanni kusan shida a gidajen kurkukun kasar daban-daban. Sai dai matakin bai shafi mai dakin tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Malam Hama Amadu ba wacce ke ci gaba da kasancewa a tsare, abin da kuma ya soma haifar da ce-ce kuce a kasar. Wasu na cewa matakin na kara tabbatar da bita da kullin siyasa da gwamnatin ke yi wa shugaban majalisar dokokin ba wai don batun cinikin jariran gaskiya ba ne. Wakilinmu a Yamai Gazali Abdou Tasawa ya ruwaito cewa, yayin wani taron manema labarai da ya kira da yammacin wannan Talata babban alkalin gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar a kotun daukaka kara Mai shari'a Ibrahim Bubacar Zakaria ya ce matakin ba shi da wata nasaba da batun siyasa kuma matar tsohon shugaban majalisar dokokin ba ta daga cikin jerin mutanen da suka aje takardar neman beli. Sai dai lauyan matar Hama Amadu ya ce ya shigar da takardar neman belin a cikin watan Oktoban da ya gabata ba tare da samun biyan bukata ba.

Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa/Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal