1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariár Milosevic a Kotun MDD

February 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6q

Kotun ƙasa da ƙasa dake shariár laifukan yaƙi wadda ke da mazaunin ta a birnin Hague ta yi watsi da buƙatar da tsohon shugaban ƙasar Sabiya Slobodon Milosevic ya gabatar mata ta neman a sako shi daga inda yake tsare a kasar Netherland domin zuwa a duba lafiyar sa a ƙasar Rasha. A wata sanarwa da kotun ta bayar ta ƙin amincewa da bukatar ta baiyana cewa babu tabbas idan aka bashi wannan dama zai dawo domin cigaba da shariar. To amma kotun tace likitocin dake duba lafiyar Milosevic wanda ke fama da ciwon zuciya da hawan jini suna iya duba lafiyar sa a kasar ta Netherland. Likitocin dake duba shi sun baiyana cewa rayuwar Milosevic na hadari.