Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 31.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka

"Hakuri da Baba go slow." wannan shine taken sharhin da jaridar die tageszeitung ta yi bayan rantsar da shugaban kasar Muhammadu Buhari a wa’adin mulki karo na biyu.

"Hakuri da Baba go slow."

A Najeriya an sake rantsar da shugaban kasar Muhammadu Buhari a wa’adin mulki karo na biyu.

Jaridar die tageszeitung ta ce an rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo a safiyar ranar Laraba, a dandalin Eagle Square a Abuja na tsahon wasu shekaru hudu masu zuwa. Baki dayansu an sake zabar su ne a karkashin jam'iyyar (APC) mai mulki cikin watan Fabarairun 2019. An kawata babban birnin Najeriyar. Sai dai tun kafin ranar rantsuwar gwamnati ta jaddad cewa ba za a yi wani gagarumin biki ba, koda yake dama ba kowa ke zumudin ganin ranar ba, domin da wahala ka ga alluna masu dauke da hotunan goyon baya.

A yankin Arewacin Najeriya inda Buhari ya fito, zai wahala kaji ana zancen rantuswar. Akwai kalubalen tsaro na mayakan Boko Haram da wani bangarensu ke kara karfi a jihar Borno, koda yake gwamnati na ikirarin samun galaba akansu. Baya ga wannan akwai matsalar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihohin Kaduna da Zamfara da kuma Katsina. Shekaru hudun da suka gabata, Buhari bai bayyana sunan ministocin da zai nada ba har sai cikin watan Octoba, abin da ya sanya aka lakaba masa suna Baba go slow, yanzu abin jira shi ne lokacin da zai sake bayyana sunan ministocinsa a sabuwar gwamnatin.

Kasuwanci mara shige a Afirka

Nairobi Gikomba Second-Hand Markt (picture-alliance/dpa/D. Irungu)

Wata kasuwa a birnin Nairobin kasar Kenya

Jaridar die tageszeitung ta ce tsarin kasuwanci mara shinge na kasashen Afirka wato "Africa Continental Free Trade Area" wani gagarumin ci-gaba ne a tarihi, sai dai akwai aiki a gaba kafin kasuwancin mara shinge a Afirkan ya ja hankali. A ranar Alhamis ne aka fara aiki da kasuwancin mara shingen a Afirka a hukumance. Yankin da aka ware domin gudanar da kasauwancin mara shingen a Afirka na zaman babar kasuwar bai daya a duniya. Idan aka kammala ta, baki dayan al'ummar kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Afirka 55 da yawaansu ya kai kimanin miliyan 1000 da miliyan 200 za su yi zirga-zirga a tsakanin kasashen ba tare da tarnaki ba. A shekara ta 2012 ne dai kungiyar ta AU ta kudiri aniyar fara kasuwanci mara shinge a tsakanin kasashen Afirkan cikin shekaru biyar da nufin sake matso da kasashen nahiyar kusa da juna. A yayin taron da kungiyar ta AU ta gudanar a Ruwanda a shekara ta 2018 kasashe 44 cikin 55 na kungiyar suka sanya hannu kan yarjejeniyar kasauwancin mara shinge. Sai dai kawo yanzu yawancin kasashen kungiyar ta AU da suka sanya hannu kan yarjejeniyar ya karu zuwa 52 yayin da kasashen Najeriya da Benin da Iritiriya suka rage basu sanya hannu akan yarjejeniyar ba.

Nasarar yaki da zazzabin cizon sauro

Anopheles stephensi Moskito Mücke (picture-alliance/dpa/J.Gathany)

Sauro mai sanya kwayar cutar maleriya

Karamar nasara a kan mai kisa, kasashe biyu sun kawar da cutar zazzabin cizon sauro na Malaria In ji jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ce cikin watan Nuwambar shekara ta 1880 ne wani likitan sojoji dan kasar Faransa Alphonse Laveran ya gano kwayar cutar a lokacin da yake aiki a kasar Aljeriya. Wannan tarihin dai ya bayar da kyakkyawan sakamako, bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa kasar ta Aljeriya ta kawo karshen cutar ta maleriya, akalla tsahon shekaru uku da suka gabata babu rahoton kamuwa da cutar a kasar. A baya dai kasashen Mauritius da Morocco kadai suka kai ga cimma wannan nasarar a Afirka. Tun a shekarar 1955 kwararru ke fatan kawo karshen kwayar cutar zazzabin cizon sauron, sai dai har kawo yanzu a kasashe 38 ne kacal suka samu cimma nasara a duniya, yayin da kasashe 80 ke fama da cutar ta malariya da mafi akasari ta fi yin illa ga kananan yara. Cutar dai kan haddasa jijjiga da zazzafan zazzabi da karancin jini.  A shekara ta 2017, an samu rahoton wadanda suka kamu da cutar kimanin miliyan 219 a duniya baki daya, inda ta hallaka mutane dubu 435 abin da ke nuni da cewa sama da mutane 1000 ke mutuwa a kowace rana.

Sauti da bidiyo akan labarin