Sharhuna kan rikicin Shi′a a Najeriya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 18.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhuna kan rikicin Shi'a a Najeriya

Rikicin sojojin Najeriya da 'yan Shi'a da rigingimu na siyasa a Burundi su ne suka fi daukar hankalin wasu jaridun na Jamus a wannan Mako mai karewa.

A sharhin da jaridar Neue Zürcher Zeitung mai taken" dumbin mace-mace sakamakon mummunan arangama tsakanin 'yan Shi'a da sojojin Najeriya" ta yi, cewa ta ke, mabiya darikar Shi'a dai daidaiku a yankin yammacin Afirka, sai dai a yankin arewacin Najeriyada ke fama da rigingimu a kwaisu. A yanzu haka suna tsinci kansu cikin wani yamutsi da jami'an tsaro sakamakon tare hanya da suka yi, kamar yadda suka saba batu da ya jagoracesu zargin kisan gillan mabiyansu.

'Yan Shi'an dai suna ci gaba da gudanar da znga zanga a kan tituna a biranen arewacin Najeriyar, inda ko a ranar Talatar da ta gabata sai da 'yan sanda suka yi ta harba musu hayaki mai sa hawaye a garin Kaduna, inad rahotanni suka ce a kalla mutane hudu sun rasa rayukansu. Daura da mutane 60 da suka rasa rayukansu a rikicin daya barke tsakaninsuda sojojin kasar a karshen makon daya gabata a garin Zaria da ke jihar ta Kaduna. Jaridar ta ce har yanzu akwai sabanin bayani dangane da zargin da bangarorin biyu kewa juna.

An dauki tsawon shekaru dai ana takun saka tsakanin mabiya darikar shi'an da jami'an tsaro, inda ko a bara yamutsin da ya barke lokacin ibadarsu ya jagoranci kashe 'ya'yan shugabansu Ibrahim Zakzaky guda uku. Kafofin yada labarun Najeriyadai sun sanar da cewar Zakzakyn ya na cikin hali mawuyaci na jinya daga harbin bindiga hudu dasojojin suka i masa ranar Asabar, kafin su yi awaon gaba da shi.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi sajojin kasar Burundi na cigaba da kashe 'yan adawa da tazarce karo na uku na shugaban kasar. A dare daya acewar jaridar, mutane 90 aka yi wa kisan gilla. Ba bakon abu ne a yanzu haka ganin yadda gawarwaki suka mamaye titunan babban birnin kasar watau Bujumbura. Sojojin sun yi nuni da cewar 80 daga cikin mutane 90 da aka kashe mayakan sakai ne da suka yi yunkurin kai wa sansanin sojoji farmaki. Sai dai wadanda suka gane wa idanunsu sun shaidar dacewar, dojoji da 'yan sandan na kashe har mutanen da bausu dauke da wani makami. A ya yin aka bi wasu har gidajensu anan bindigesu, musamman unguwannin da 'yan adawa suka fi yawa.

Rikicin na daren juma'a zuwa wayewar garin Asabar dai ya kasance mafi munin irinsa tun da aka fara rikicin siyasar kasar ta Burundi. 'Yan adawar kasar dai sun fara ne da zanga zangar lumana na adawa da tazarcen shugaba Nkurunziza a karo na uku, batu da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Daga nan ne yasa aka afkawa masu gangamin da karfin soji, batu da har ya zuwa yanzu ya ke ci gaba da ta'azzara.

A kasar Afirka ta kudu kuwa acewar jaridar Süddeatsche Zeitung, ba za'a mance da zargin sama da fadi da dukiyar kasa da aka yi wa shugaba Jacob Zuma da mukarrabansa ba. Yadda ya yi amfani da kudaden haraji wajen yin garon bawul din gidansa, da kuma gazawar gwamnati wajen shawo kan matsalolin rashin aikin yi da matsi na tattali da jama'a ke fama da su.Wadannan dai sanannun matsaloli ne a Afirka ta kudu a tun a watan Mayun shekara ta 2014, lokacin da aka gudanar da zaben kasar. Sai dai duk da haka jam'iyyar ANC mai mulki ta samu kashi 62.

A cewar al'ummar kasar dai ba Jacob Zuma suka zaba ba, sun zabi jam'iyyar ANC ce, wadda ta kwato musu 'yancinsu da kuma wata irin kima da darajawa marigayi Nelson Mandela. Ko yara da aka haifa bayan kawo karshen mulikin nuna wariyar launin fata a Afirka ta kudun dai na alfahari da jam'iyyarta ANC. Duk yunkurin da jam'iyyar adawa da AD ta yi na ganin cewar ta taka rawa a zaben bai kaita ga yin nasarar da ya shige samun kashi 22 daga cikin 100 ba.