1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Sharhin jaridun Jamus kan kasashen Afirka

Usman Shehu Usman MAB
September 13, 2024

Iftila'in ambaliyar ruwa a Maiduguri na Najeriya ya dauki hankalin jaridun Jamus, baya ga rikicin Habasha da Somaliya da ke kara ta'azzara da kuma yadda cutar kyandar biri ke addabar wasu kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/4kbZ5
Matasa sun rinka taimaka wa masu yawan shekaru sakamakon ambaliya a Maiduguri
Matasa sun rinka taimaka wa masu yawan shekaru sakamakon ambaliya a MaiduguriHoto: AUDU MARTE/AFP

Jaridar Süddeutscher Zeitung ta ce wani mummunar ambaliyar ruwa a Najeriya ta sa yara da iyalan kwana a filin Allah, lamarin da ke.  kungiyoyi shelar kawo agajin gaggawa. Ruwan sama mai karfi hadi da ballewar madatsar ruwa sun jawo kwararar ruwa cikin gidajen jama'a a daren Talata, inda a birnin Maiduguri ga misali, yara kanana da iyayensu sun samu kansu a fili sakamkon ambaliyar da ta ratsa babbar birnin jihar Borno. Süddeutscher Zeitung ta ce tun daga karshen watan Agusta ne aka samu barnar amabaliyar ruwa har i zuwa kasashe makwabtan Najeriya kamar Jamhuriyar Nijar, haka har izuwa kasar Mali ma, ruwan sama ya yi matukar barnar gidaje da amfanin gonaki.

Sakamakon zaben Aljeriya ya sha fassara

Abdelmadjid Tebboune ya nuna farin ciki bayan da ya sake lashe zaben Aljeriya
Abdelmadjid Tebboune ya nuna farin ciki bayan da ya sake lashe zaben AljeriyaHoto: Photoshot/picture alliance

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi waiwaye ne kan zaben shugaban kasa a Aljeriya, inda jaridar ta ce an samu karancin fitowar masu kada kuri‘a a zaben shugaban kasa.  Ya zuwa yanzu dai, ko an fito da yawa ko kuma ba a fito ba, amma ta tabbata shugaba mai ci Abdelmadjid Tebboune zai dore kan mulki na akalla sabon wa'adin shekaru biyar, domin kuwa sanarwar da Mohamed Charfi da ke zama shugaban hukumar zaben Aljeriya ya fitar ta nuna cewa Shugaba Tebboune ya samu kashi 94% na kuri'un da aka kada. Sauran 'yan adawa da suka yi takara sun samu kashi 2% zuwa kashi 3& na yawan kuri'un da aka kada.

Habasha na ci gaba da takaddama da makwabtanta

Faretin sojojin Habasha a daidai lokacin da kasar ke rikici da Somaliya
Faretin sojojin Habasha a daidai lokacin da kasar ke rikici da SomaliyaHoto: Mesay Teklu/DW

Die Tageszeitung ta ce kasar Habasha na bikin samun 'yancin kai, yayin da rikicin kasar da Somaliya ke ruruwa. Jaridar na mai cewa a yayin da Firaminista Abiy Ahmed ke halartar faretin ban girma a ranar samun 'yancin kai, ya yi amfani da wannan dama wajen gargadin makwabtan kasar da yake shugabanta. A kwanakinan dai, rikici tsakanin Somaliya da Habasha ya kara bude sabon babi, lamarin da ya sa kasar Masar jibge dakarunta a kusa da iyakarsu da Habasha, kuma a cewar Masar, ta zo kusa da Habasha ne bisa gayyatar kasar Somaliya, saboda Somaliya na da tsamin dagantaka da makwabciyarta a bisa yunkurin Habasha na amincewa da yancin Somaliland a matsayin kasa mai 'yanci. Dama kuma akwai babbar matsala tsakanin Masar da Habasha, musamman kan batun  madatsar ruwan samar da lantarki.

Cutar kyandar biri ya dauki hankalin jaridun Jamus

Cutar kyandar biri na yaduwa a wasu kaashen Afirka sakamakon rashin rigakafi
Cutar kyandar biri na yaduwa a wasu kaashen Afirka sakamakon rashin rigakafiHoto: WHO/Aton Chile/IMAGO

Sharhin jaridar die Zeit ya dubi yadda cutar kyandar biri ke kara yaduwa a Afirka. Jaridar ta ce hukumar kula da cututtuka masu saurin yaduwa ta Afirka ta sanar da yadda kyandar biri ke yaduwa cikin kasashen nahiyar cikin Sauri. Inda hukmar ta ce a kwanaki bakwai kacal, an samu labarin mutane 5.466 sabbin kamuwa da kyandar biri, kuma mutane 26 ne suka mutu sakamakon cutar. A tsakiyar watan Augustan 2024, kasa da mutane 1.400 ne suka kamu da cutar, wanda ya yi kasa matuka idan aka kwatanta da wadanda suka kamu da cutar a wannan makon farko bayan bullarta. Jaridar ta ce tun farko bana i zuwa yanzu, mutane 25,000 ne aka bayar da rahoton kamuwarsu da cutar kyandar biri, amma kuma babbar matsalar da ake samu wajen gaggauta yin gwaji, ita ce rashin wadattatun wuraren binciken cututtuka a Afirka.