1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka da yakin Rasha cikin jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 11, 2022

Yakin da ake tsakanin Rasha da Ukraine da ke shafar wasu kasashen Afirka, ya dauki hankulan Jaridun Jamus na wannan makon.

https://p.dw.com/p/48Njl
Ukraine-Rikici - Majalisar Dinkin Duniya-Kwamitin Sulhu
Yayin da kasashen Turai suka amince da kudirin yin tir da Rasha, wau na Afirka sun kiHoto: John Minchillo/AP/dpa/picture alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cikin sharhinta mai taken: "Tasirin Rasha. Kasashen Afirka da dama sun kauracewa kada kuri'unsu kan yin tir da hare-haren da Rasha ke kai wa  a Ukraine a yayin taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya, ko mai yasa?" Jaridar ta ce a karshe wadanda suka yi yaki da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, sun nuna kin amincewarsu. A cewarsu taimakon da tsohuwar Tarayyar Soviet ta ba su, ba zai saka su gaza sukan matakin Rasha a Ukraine na yanzu ba. Cikin wani koke da wata kungiya ta rubuta, ta nunar da cewa taimaka musu da aka yi, ba zai sa su goyi bayan rashin adalci ba. Duk da cewa Afirka ta Kudu na cikin kungiyar Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Habaka wato BRICS da suka hadar da Brazil da Rasha da Indiya da Chaina da kuma ita Afirka ta Kudun, a ranar Larabar da ta gabata kasar na cikin kasashe 35 da suka yi rowar kuri'unsu yayin kuri'ar yin tir da hare-haren Rasha a Ukraine da aka kada a Majalisar Dinkin Duniya. Ana ganin dai matakin da sauran kasashen Afirka suka dauka na yin rowar kuri'unsu ko kuma kauracewa kada kuri'ar, ba ya rasa nasaba da taimakon da tsohuwar Tarayyar Soviet ta ba su da kuma yadda a baya-bayan nan Rashan ke taka rawa a harkokin tattalin arziki da ma dangantakar soja a Afirkan.

Turkiyya I Burodi
Duniya dai na shirin fuskantar karancin abinci, musamman ma burodiHoto: Adem Alta/AFP

Ita kuwa jaridar die tages zeitung ta rubuta sharhi ne mai taken: "Dandana kuda sakamakon yakin da ake a Turai. Yaki ya shafi kwaryar burodi a duniya." Jaridar ta ce yayin da aka samu tangarda wajen fitar da alkama daga kasashen Ukraine da Rasha, fannin abinci a kasashen gabashin Afirka na fuskantar barazana. Ta ce yakin da ake a Ukraine, ka iya kara ta'azzara matsalar abinci a gabashin Afirka. A dangane da haka Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa, a yanzu haka akwai sama da mutane miliyan 283 da ke fama da matsalar yunwa kuma wasu miliyan 45 na fuskantar barazana. Jairdar ta ce, Babbar Matsalar ita ce: Kasar Ukraine da ke yankin Tekun Bahar Maliya, daga nan ne kaso 18 cikin 100 na alkamar da ake samarwa a duniya ke fitowa yayin da kaso 40 na man girki yake fitowa daga can. Haka kuma daga wannan yanki ne dai, ake fito da kaso 14 cikin 100 na masara a duniya. Rashin fito da wadannan kayan abinci daga wannan yanki, ya janyo farashi ya yi tashin gauron zabi a kasuwannin sayar da kayan abinci na duniya. A yanzu haka tuni alkama ta yi tsadar ta ba ta taba yi ba. Kasashen da wannan matsala za ta fi shafa su ne na yankin gabashi da kuma Kahon Afirka: Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu da Kenya da Habasha sun fi fuskantar gagarumar barazanar yunwar, sakamakon karancin ruwan sama saboda matsalar sauyi ko dumamar yanayi. Koda yake a yankin gabashin Afirka akwai wadatar alkamar a kasuwanni kawo yanzu, sai dai tarin matsaloli musamman ma na tattalin arziki sakamakon annobar corona na barazana.

Kwantena I BioNTech I Marburg
Kamfanin BioNTech, na shirin kara fadada harkokinsa a AfirkaHoto: FABIAN BIMMER/REUTERS

Za mu karkare da sharhin jaridar Handelsblatt mai taken: Moderna ta fadada kasuwancin BIOTECH zuwa Afirka. Jaridar ta ce, sabuwar allurar riga-kafi kan cututtuka a Afirka da kuma kafa kamfani a kasar Kenya. Da haka ne kamfanin na Moderna, ke son fadada harkokinsa a Afirka. Kamfanin samar da allurar riga-kafin na Amirka, na kara karfin ayyukansa na yaki da annobar a kasashe masu tasowa. Kamfanin zai kashe kimanin dalar Amirka miliyan 500, wajen kafa sabon reshensa a kasar Kenya. Haka kuma, yana shirin samar da gagarumin tsarin bincike. A ranar Litinin din da ta gabata ne, kamfanin na Moderna ya sanar da cewa zai kafa kamfanonin bincike kan cututtuka masu yaduwa guda 15, nan da shekara ta 2025 a kasashen Afirkan. Cututtukan da binciken zai mayar da hankali, sun hadar da cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDs ko kuma SIDA da Tarin Fuka da Ebola da kuma zazzabin Lassa.