Sharhin Jaridun Jamus a kan nahiyar Afrika
August 30, 2024Jaridar FAZ ta ce hari ya hallaka gomman mutane a kasar Burkina Faso, ciki har da mata da yara kanana da kuma tsofaffi, sai dai jaridar ta ce abun kaicho ba wanda ya dauki alhakin harin. Kawai dai batu daya a hukumance wanda aka ji shi ne wani ministan gwamnatin ya bayyanan cewa wasu yan bindiga sun hallaka mutane da yawa, amma bai yi karin haske ba. An dai kai dararuruwan mutanen da suka jikkata asibiti.
Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta duba wani rikici da ke tasowa tsakanin Kasar Habasha da Masar. Jaridar ta ce yaki bisa takaddamar ruwa a tsakiyan hamadar Somaliya. Tun shekarun da suka gabata ne ake samun takaddama tsakanin Masar da Habasha kan babbar tashar mamakamashi da Habasha ta gina kan Kogin Nilu. Amma yanzu rikicin kasashen na Habasha da Masar ya tashi daga batun madatsar ruwa izuwa cikin kasar Somaliya. Bisa rahotrannin da aka bayar kasar Masar ta tura kimanin dakarun soja 10,000 cikin Somaliya, yayin da ita ma Habasha aka ruwaito ta shirya tura nata dakarun izuwa Somaliya. Ita dai Somaliya ta gayyaci sojan Masar ne biyo korafinta kan yadda Habasha ke son kulla hulda da yankin Somaliland, wanda Somaliya ke dauka wani baggaren kasarta ne.
Jaridar Süddeutsche ta ce kashen Yamma sun fara aika riga-kafin kyandar biri izuwa Afirka. Jaridar ta ce a yan watannin baya da wuya ka jin batun cutar kyandar biri a kasashen Yamma, amma kuma tuni har sun samar da allurar riga-kafin cutar wacce a watan da ya gabata aka fara bayyana cutar a matsayi barazana ga duniya. Tarayyar Turai ita kadai ta aika da allurai 175,000 izuwa kasashen tsakiyar Afirka wadanda matsalar ta fi kamari, sai kasar Amurka wace ta aika da allurai 50,000 yayin da kasar Faransa ta aike da allurai 100,000. Kasar Japan ta sanar da shirin aika nata taimakon haka kuma wasu kasashen suma suna kan hanyar tura riga-kafin cutar ta kyandar biri.
A sharhinta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba arziki daga indallahi wanda ya bulla a kasar Botswana. Inda ta ce a kasar ta Botsawa an samu dutsen lu'u-lu'u mai nauyin Gram 500 wanda aka kyasta kudinsa ya kai Euro milian 40. A cewar jaridar wani mai suna Frederick Wells- shi ne ya taba gano irin wannan dutsen Lu'u-lu'u mafi girma duniya. Wato a shekara ta 1905 lokacin da dan kasar ta Birtaniya ya kai ziyara daular Botsawana ya gano dutsen Lu'u-lu'u mai nauyin gram 620. Wannan dai wata dama ce ta tabbatar wa Botsawana tana da arzikin karkashin kasa. Kuma dama kasar Botsawana ta kasance kasar da ke kan gaba a dorewar mulkin demokradiya mai tsabta.