1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: rashin damawa da matasa a Afirka

Claus Stäcker MAB
December 7, 2017

Shugaban sashen Afirka na DW, Claus Stäcker, ya bayyana a cikin sharhin da ya yi cewa ba a cika damawa da matasa a Afirka ba duk da kwazo da shi. Wannan ya zo a daidai lokacin da muka kaddamar da sabon shirin Matasa Kashi 77.

https://p.dw.com/p/2ox6k

Kashi  77 cikin 100* na al'ummar Afirka Kudu da Hamadar Sahara matasa ne da ba su haura shekaru 35 ba. Suna zuwa makaranta, suna neman ilimi a jami'a suna kuma neman aiki. Suna son yin aure, suna son daukar nauyin kansu. Suna hulda da junansu a shafukan sada zumunta na Facebook da WhatsApp da Instagram. Sun gane cewa suna da rinjaye na kashi uku cikin hudu, amma ba a ba su damar tofa albarkacin bakinsu. Ba a mayar da hankali kan damuwarsu. ‘Yan siyasa ba sa daukar batunsu da wani muhimmanci.

Sau da yawa tsofaffi ne ke jan ragamar mulki. Robert Mugabe a Zimbabuwe yana da shekaru 93 kafin ya yi murabus. Ya kasa magance matsalolin matasan. Matasan Afirka masu kwazo ne da hazaka ga su kuma da basira, amma ba su da wata makoma ta a zo a gani. Shin ko ‘yan siyasa na ba da himma wajen duba  bukatunsu?

Dogon buri da hangen samun wata rayuwa mai kyau na ingiza matasa da yawa zuwa Turai ko Afirka ta Kudu ko wasu kasashen duniya, suna bin haramtattun hanyoyi masu hatsari don neman biyan bukata. A cikin shirye-shiryenta da muhawarori a shafukan sada zumunta, tashar DW tana tabo matsaloli da kuma fata na matasa. A muhawarori da ta gabatar a biranen Abidjan da Accra da Bamako da Banjul da Konakry da Dakar da Jos da kuma Yamai, DW tare da hadin gwiwa da tashoshin rediyo da ke hulda da ita sun tattauna da matasa da ‘yan siyasa a kan batun hijira karkashin taken ‘‘Hangen Dala…" Muhawarorin sun kasance masu zafi da sosa rai da kuma daure kai. Ya dai bayyana a fili bukatar tattaunawa da juna, a yi musayar ra‘ayi a kuma mika damuwar matasan ga wadanda alhaki ya rataya a wuyansu. Wannan shiri da a Turancin Ingilishi aka yi wa lakabi da ‘‘The 77percent" wato ‘‘Matasan Afirka kashi 77 ne" zai kasance wani babban dandali na musayar ra'ayoyi a shafukan sada zumunta da rediyo da kuma telebijin.