Sharhi: Nahiyar Turai tana jan-kafa a rikicin Mali | Siyasa | DW | 18.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Nahiyar Turai tana jan-kafa a rikicin Mali

Batun tsaro a kasar Mali al'amari ne da ba nahiyar Afirka kadai ya shafa ba, amma har da nahiyar Turai

Kasashen Turai kawayen Faransa bayan jan-kafa na lokaci mai tsawo, yanzu dai sun daidaita a game da taimakon da zasu iya baiwa Faransa da kuma kasar Mali, a kokarin da suke yi na kawo karshen mamayewar da yan tawaye suke yiwa yankunan kasar. Kasashen na Turai sun sanar da cewar zasu tura jami'ai 250 da zasu horad da sojojin Mali, yadda zasu iya kare kasar daga yan tawaye musulmi.

Kasashen Turai, inji Ute Schaeffer da ta rubuta wannan sharhi, sai da suka dauki tsawon wata da watanni kafin su yanke shawara, inda kafin su kai ga hakan, kungiyoyin na musumi, dauke da burinsu na shimfida shari'ar musulunci, suka ci gaba da mamaye kauyuka da garuruwan arewacin Mali, suna tsoratar da mazauna yankin, ta hanyar kashe-kashe, fyade, azabtarwa a wannan kasa kasa da ta taba zama abin misali ga tafarkin demokradiya a nahiyar Afirka baki daya. Faransa ta kai ganon cewar halin da Malin take ciki ba abu ne da za'a iya shawo kansa ta amfani da dabarun siyaa ba, yayin da sauran nahiyar Turai suka zura idanu ko suke ta nazarin abin da ya dace suyi kan kasar ta Mali. Al'ummar Faransa kuma suna nuna cikakken goyon bayansu ga wannan mataki da gwamnatinsu take yi a Mali, tare da izini da goyon bayan majalisar dinkin duniya.

Deutsche Welle Chefredakteurin Ute Schaeffer altes Format

Babbar editan DW Ute Schaeffer

Sai dai ita kuma Jamus fa? Shekara guda kafin babban zaben kasar, yan siyasa sun baiyana sha'awar kaucewa tabo duk wani abin da ya shafi rikicin Mali, saboda hakan yana iya tayar da muhawara mai yawa tsakanin al'ummar kasa. Hakan ya sanya Jamus din taki shiga sosai a wannan rikici, inda ta yanke shawarar tura jiragen saman soja biyu ne kawai na daukar kaya domin taimakon Faransa. Duk wani abin da ya wuce haka, misali tura sosai a wannan riikici, tilas ya sami amincewa daga majalisar dokoki, abin da zai shiga kanun labarai ya tada muhawarar da ake tsoro tsakanin jama'a. Ga kafofin yada labaran Jamus, Mali dai bata wuce kasa ta hamada a yankin Sahel ba. To amma tana iya kasancewa kasar da zata zama tushen rikici-rikice da tashin hankali a nahiyar baki daya, saboda idan har Mali din ta rushe yankin Sahel yana iya cin wuta gaba dayansa, abin da zai shafi Jamus da nahiyar Turai a matsayin makwabtan juna. Mali a matsayin daya daga cikin kasashen da suka fi girma a Afrika, tana da iyaka da kasashe bakwai, wadanda da yawa daga cikinsu kasashe ne masu matukar rauni, dake fama da matsaloli irin nata, kamar talauci da rashin mulki na-gari da kungiyoyi na yan tarzoma da aikata manyan laifuka.

Wajibi ne kuma ayi magana game da hadarin dake tattare da tura sojoji a rikicin na Mali, musamman sojojin kasa, inda sojojin Faransa suke samun taimako daga dakarun kungiyar ECOWAS kimanin 3300. Sai dai hadarin da za'a fuskanta idan har ba'a dauki wani mataki yanzu ba a Malin zai fi zama mai muni. Ana iya ganin alamun haka daga abin da ya faru na kame yan kasashen ketare da ake garkuwa dasu a wani wurin samar da gas a kudancin Aljeriya, abin da ake dora alhakinsa kan yan kungiyar al-Qaeda na arewacin Afirka dake neman Faransa ta kawo karshen aiyukan ta na soja a Mali.

Nigerianische Truppen bereiten sich auf Einsatz in Mali vor

Sojojin Najeriya sun isa Mali

Abin tambaya shine: shin nahiyar Turai zata zura ido tana ganin yadda ake kokarin kafa kasa ta shari'ar musulunci a Mali? Shin kasashen Turai sun yi imanin cewar ta hanyar zura ido ko kawar da idanun su daga rikicin, zai kawo a shawo kan matsalar ta Mali? Ana bukatar daukar mataki mai karfi da zai tabbatar da sake maida kasar ta Mali bisa tafarki na tsaro da baiwa jama'a damar tafiyarda rayuwa mafi dacewa da kaucewa halin kaka-ni-kayi. Idan kuwa hakan bai samu ba, za'a iya shiga barazanar da kungiyoyin yan tarzoman na yankin Sahel zasu hade da takwarorin su kungiyoyin musulmi masu matsanancin ra'ayi a yankin gabashin nahiyar ta Afrika, a kahon Afirka da Kenya, abin da zai haifar da mummunan sakamako ga nahiyar Turai.

Mawallafi: Ute Schaeffer/Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin