Sharhi: Mursi ya nemi hanyar yin sulhu | Siyasa | DW | 07.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Mursi ya nemi hanyar yin sulhu

Rikici tsakanin jam'iyyun adawa da shugaba Mursi na cigaba da ɗaukar wani salo bayan da aka fidda daftarin kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma ƙarin ƙarfin iko da Mursi ya ba kansa.

Tashe tashen hankulan baya-bayan nan sun faro ne bayan da shugaba Mohammed Mursi ya ba wa kansa karin iko da bisa ga dukkan alamu ya kawar da batun raba madafun iko a ƙasar. Ya yi amfani da sabuwar dokar wajen rage ƙarfin ikon ɓangaren shari'a na ƙalubalantar duk wani mataki da ya ɗauka.

Mursi ya na da ƙwararan dalilai na yin haka domin kotun kare kundin tsarin mulkin ƙasar na zaman wata hukuma ta ƙarshe da aka gada daga tsohuwar gwamnatin Hosni Mubarak. Wannan kotu ce kuma ta zama 'yar amshin shatar sojojin ƙasar da yanzu su ka rasa iko. A cikin watan Yuni kotun ta soke zaɓen 'yan majalisar dokoki da aka gudanar cikin gaskiya da adalci.

Ägypten Proteste auf dem Tahrir-Platz in Kairo

Masu zanga-zanga a dandalin Tahrir

Mursi ya yi zaton kotun tsarin mulkin za ta rusa majalisar dokoki mai rinjayen wakilan 'yan uwa Musulmi. Sai dai da wannan mataki ya mayar da hannun agogo baya ga sauye-sauyen da ake yi bayan juyin juya hali wanda kuma da zai yi mummunan tasiri ga harkokin siyasar ƙasar ta Masar.

Mursi ke da laifin taɓarbarewar al'amura a cikin ƙasar saboda rashin hangen nesan sa. Da kamata ya yi ya nemi tattaunawa da masu zanga-zanga a dandalin Tahrir kuma ya gode musu saboda dalilinsu ya lashe zaɓe. Maimamkon haka sai ya ƙara wa kansa ikon zama ɗan mulkin kama karya kuma dogara ga tsarin mulki ba tare da ya ƙarfafa goyon baya ba.

Sai dai Mursi ba Fir'auna ba ne kana ba sabon Mubarak ba ne. Shi ne zaɓaɓɓe kuma halastaccen shugaba na demokraɗiyya a Masar. An yi gaggawa wajen fasalta daftarin kundin tsarin mulkin da Misrawa za su kaɗa ƙuri'a kansa a tsakiyar wannann wata. Idan aka dubi kalmomin da ke ciki za a ga cewa bai ƙunshi wasu abubuwa da zai sa masu sassaucin ra'ayi a ƙasar zargin cewa ana shirin kafa wata daular Islama ce shigen ta Iran.

Loay Mudhoon

Mursi ya nemi hanyar yin sulhu in ji Loay Mudhoon

Daftarin cewa ya yi Musulunci zai zama ƙashin bayan dokokin ƙasar, wannan kuwa ba sabo ba ne kuma ba wani abu ne mai haɗari ba. domin tun a shekarar 1971 wannan sashe ke zaman wani ɓangare na tsarin mulkin Masar kuma masu sassaucin ra'ayi da Musulmi masu rajin sauyi na magana game da matakin ƙarshe na shari'ar musulunci ne idan suna son haɗe salon demokraɗiyyarsu da addinin Islama.

Bugu da ƙari daftarin kundin tsarin mulkin ya tabbatar da 'yanci dai-dai wa daida ga dukkan 'yan ƙasar a gaban shari'a ba tare da 'yancin 'yan jarida da faɗi albarkacin baki. Sai dai abin takaici ba a fito ƙarara aka bayyana 'yancin mata da tsiraru ba, in ban da muhimmancin iyali a Masar da aka jaddada. Kazalika an taƙaita wa'adin shugabanci ya zuwa sau biyu.

Saboda haka rikicin da ake yanzu ya wuce na adawa da ƙarin iko da Mursi ya ba wa kansa da kuma daftarin tsarin mulkin ba. Rikicin dai na da nasaba da sabon yanayin da aka shiga a Masar, musamman rashinn jituwa tsakanin masu sassaucin ra'ayi da musulmi masu ra'ayin mazan jiya dake da rinjaye a ƙasar. Da wataƙila wannan rukunin na jama'a sun goyi bayan Mursi in da ya nemi tattaunawa da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa. Dole ne Mursi ya nemi hanayar sasantawa.

Mawallafa : Loay Mudhoon/Muhammad Nasir Awal
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin